Kaduna: 'Yan bindiga sun sako dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist

  • Masu garkuwa da mutane sun kara sakin dalibai 32 ‘yan makarantar Bathel Baptist da ke jihar Kaduna
  • Joseph Hayab, shugaban CAN na reshen jihar Kaduna ne ya sanar da hakan ranar Juma’a hakan
  • A cewar Hayab, tuni suka koma wurin iyayensu duk da dai bai yi karin bayani a kan lamarin ba

Kaduna - An kara sako dalibai 32 daga cikin daliban makarantar Bathel Baptist da ke Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Joseph Hayab, shugaban kungiyar Kiristoci na reshen jihar Kaduna ya tabbatar da sakinsu a ranar Juma’a.

An kara sakin dalibai 32 da yamman nan, a cewarsa.

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist
Kaduna: 'Yan bindiga sun sako dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara

Hayab ya ce daliban sun koma wurin iyayensu, duk da dai bai fadada bayanan ba.

An samu wannan cigaban ne bayan kwana daya da sako daliban Islamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina jihar Neja bayan sun kwashe kwanaki 88 a hannun masu garkuwa da mutane.

Yanzu haka akwai dalibai 31 da suke hannun masu garkuwa da mutanen.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel