An yi kicibis: Kwankwaso da Ganduje sun ajiye gabar siyasa, sun dawo Kano tare daga Abuja

An yi kicibis: Kwankwaso da Ganduje sun ajiye gabar siyasa, sun dawo Kano tare daga Abuja

Rabiu Musa Kwankwaso ya hadu Gwamna Abdullahi Ganduje a Kano

Tsohon Gwamnan ya yi ido biyu da Dr. Ganduje ne a filin jirgin Abuja

Ganduje da Kwankwaso sun hadu, jirgin samansu ya iso Kano dazu

Abuja - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun hadu a filin tashi da saukar jirgin sama da ke Abuja.

An hadu a Abuja

Jaridar Daily Trust ta ce Abdullahi Umar Ganduje ya hadu da tsohon gwamnan a filiin na Nnamdi Azikiwe a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta, 2021.

Manyan ‘yan siyasar sun hadu ne a dakin da ake zama a jira zuwan jigin sama a filin na Abuja.

Kara karanta wannan

Yadda aka jefa ni kurkuku na shekara 1 a lokacin Abacha - Sanusi ya bude faifan da ba a tabawa

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, Mai girma gwamnan ya gaisa da tsohon mai gidan na sa a dakin zaman, kafin kowa ya kama hanyar gabansa.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa jirgin da ya dauko ‘yan siyasan ya iso garin Kaduna tun da rana.

Kwankwaso da Ganduje Hoto: dailynigerian.com
Kwankwaso da Ganduje Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Bayan isowarsa Kano, Sanata Kwankwaso ya jagoranci zaman shugabannin jam’iyyar PDP na yankunan Kura, Madobi, Garun Malam da Dawakin Kudu.

Ya alakar Ganduje da Kwankwaso ta ke?

A lokacin da Rabiu Musa Kwankwaso yake gwamnan jihar Kano sau biyu, Abdullahi Umar Ganduje ne ya zama mataimakinsa, kafin ya gaje shi a 2015.

Bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nada Sanata Kwankwaso a matsayin Ministan tsaro, Ganduje yana cikin masu ba shi shawara.

Amma da Abdullahi Ganduje ya hau mulki, ya samu sabani da Rabiu Kwankwaso. Wannan rigimar ta yi sanadiyyar da kowa ya ja daga da mabiyansa.

Tun bayan da Ganduje ya raba jiha da Kwankwaso, ba a cika ganin ‘yan siyasan tare da juna ba.

Kara karanta wannan

An hallaka makiyaya 3 a wani sabon harin ramuwar gayyar 'yan bindiga a Kaduna

Haduwar ta su ta zo ne bayan an gama bikin ‘dan shugaban kasar Najeriya, Yusuf Muhammadu Buhari da gimbiyar kasar Bichi, Zahra Nasiru Ado Bayero.

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya dauko labarin daure shi da aka yi a gidan yari. Sanusi II yace an garkame shi ne saboda yana sukar soja.

Sanusi II yace sai da Mutumin da ya mika shi kurkuku ya durkusa masa da ya zama Sarkin Kano. Khalifan na Tijjaniya yace ya shafe kwanaki 333 a kukuku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel