Yadda aka jefa ni a kurkuku na shekara 1 a lokacin Abacha - Sanusi ya bude faifan da ba a tabawa

Yadda aka jefa ni a kurkuku na shekara 1 a lokacin Abacha - Sanusi ya bude faifan da ba a tabawa

  • Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya dauko labarin daure shi
  • Muhammadu Sanusi II yace an garkame shi ne saboda yana sukar mulkin soja
  • Mai martaban yake cewa hukuma ta bi ta goge cewa ya shiga gidan yari a tarihi

Abuja - A kusan karon farko, tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya bude bakinsa a kan lokacin da ya samu kansa a tsare, a hannun hukuma.

Jaridar Sahelian Times ta rahoto Muhammadu Sanusi II yana bada labarin zamansa a dakin da ‘yan sanda suke ajiye marasa gaskiya a Bompai, jihar Kano.

Bugu da kari, bayan ya samu kansa a hannun ‘yan sanda, tsohon Sarkin ya shafe kwanaki 333 a gidan kurkuku a garin Sokoto, a lokacin da yake matashinsa.

Bayan dawowar Sanusi II daga Sudan

“A lokacin da nake Sudan, ina da tsattsauran ra’ayi, ina tunanin komai ya tabarbare a lokacin.”
“Ina sukar gwamnatin soja da mulkin kama-karya, ina tare da masu kare hakkin Bil Adama da kokarin kawo cigaba, kuma a lokacin mulkin Janar Abacha ne.

Wasu daga cikin manyan gidan sarauta ba su jin dadin abin da yake yi, a lokacin ana ganin sarauta ta ba gwamnati daurin-gindi, don haka aka sa masa ido.

Sanusi
Tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II Hoto: africanarguments.org
Asali: UGC

Me ya kai Sanusi gidan maza?

“A 1995, rikicin addini ya barke a Kano, wani ya sa najasa a kan Al-Qur’ani. Babu abin da ya hada ni da lamarin. Ina masallaci a ranar, sai abin da ya faru, ya faru.”
“Ba tare da an yi shari’a, ko an fada mani laifi na ba, na yi kwana 11 a ofishin ‘yan sanda a Bompai, daga nan aka yi amfani da dokar soja, na shafe kwana 333 a kukurku a Sokoto. Bayan shekara daya a kurkuku, sai aka fito da ni”

Mai martaba yace abin mamaki, jami’an gwamnati sun yi ta kokarin goge tarihin kai shi gidan maza saboda tsoron ko zai maka su a kotu bayan ya samu ‘yanci.

Tsohon gwamnan na bankin CBN yace ya fito da fushin kowa, amma mahaifinsa ya yi masa nasiha.

Sanusi II ya kawo labarin wani kawunsa da ya mika shi a hannun ‘yan sanda a lokacin, a karshe sai da wannan mutumi ya durkusa masa.bayan ya karbi sarauta.

Muhammadu Sanusi II wanda shi ne Sarki na 14 a kasar Kano ya dauko wannan bayani ne a wajen bikin da aka shirya domin a taya shi murnar cika shekara 60.

Sultan ya cika shekara 65

Ku na da labari cewa a ranar 24 ga watan Agusta irin ta yau a shekarar 1956 aka haifi Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Mun ttsakuro kadan daga cikin tarihin Sultan domin masu bibiyar shafinmu su san rayuwar Mai alfarama Sarkin Musulmi wanda jikan Shehu Usman Danfodio ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel