Wannan ra'ayin ka ne: FG ta yi wa Masari martani kan cewa mutane su kare kansu daga ƴan bindiga

Wannan ra'ayin ka ne: FG ta yi wa Masari martani kan cewa mutane su kare kansu daga ƴan bindiga

  • Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta ce bata goyon bayan kiran da Masari ya yi na cewa mutane su tashi su kare kansu daga yan bindiga
  • Gwamnatin ta bakin Ministan Harkokin Yan sanda, Mohammed Dingyadi ya ce Masari na da ikon ya bayyana ra'ayinsa
  • Dingyadi ya ce gwamnatin tarayya ba ta goyon bayan mutane su dauki makamai ba bisa ka'ida ba sai dai samar da yan sandan unguwa

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kiran da Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina da takwararsa na Jihar Benue, Samuel Ortom, da wasu kungiyoyi da mutane suka yi na cewa mutane su kare kansu daga 'yan bindiga, rahoton Daily Trust.

Wannan ra'ayin ka ne: FG ta yi wa Masari martani kan cewa mutane su kare kansu daga ƴan bindiga
Ministan Harkokin 'Yan Sanda, Mohammed Dingyadi. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Ministan Harkokin 'Yan sanda, Mohammed Dingyadi, yayin jawabin shekara-shekara na ma'aikatarsa karo na biyu a hedkwatar yan sanda a Abuja ya ce gwamnati bata goyon bayan mutane su dauki makamai da kansu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kashi 10 na jama'ar Borno sun bace saboda Boko Haram, inji Zulum

Sannan, Ministan ya kara da cewa Masari yana da ikon fadin ra'ayinsa kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.

A cewar Dingyadi:

"Ya kamata mu sani cewa a Nigeria muke, inda kowa ke da ikon fadin ra'ayinsa. Ina tunanin gwamnan na da damar neman yin abin da ya ke ganin ya dace a jiharsa."

Amma, ya ce hakan na kan tsari idan har za a kare kai ne ta hanyar samar da 'yan sandan unguwanni don inganta tsaro.

Dingyadi, ya kuma ce kallubalen da jami'an tsaro ke fuskanta shine yakin sunkoro da yan bindigan ke yi na hari sannan su gudu amma sojojin za su magance matsalar.

A cewarsa, gwamnati da hukumomin tsaro na bukatar hadin kan al'ummar kasa da goyon baya don 'gwamnatin za ta iya magance matsalar.'

Kara karanta wannan

Ba Ni Na Fara Fadin Wannan Maganar Ba, Gwamna Ya Maida Martani Ga Masu Kiran Ya Yi Murabus

Ya cigaba da cewa ba a tsammanin mutane su kwanta ba tare da daukan matakan kare kansu ba, su kare makwabtansu da unguwanninsu, wannan shine manufar samar da yan sandan unguwanni.

"Kowa ya bada gudunmawarsa wurin yaki da laifuka. Abin da muke cewa shine kada mutane su dauki makamai ba bisa ka'ida ba."

Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

A wani labarin daban, kun ji cewa Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba kuma ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Auren dan Shugaba Buhari: Talakan Najeriya ya shiga uku – In ji Sheikh Ahmad Gumi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel