Da dumi-dumi: Kashi 10 na jama'ar Borno sun bace saboda Boko Haram, inji Zulum

Da dumi-dumi: Kashi 10 na jama'ar Borno sun bace saboda Boko Haram, inji Zulum

  • Gwamnan jihar Borno ya bayyana Boko Haram ta yi wa jihar illa cikin shekaru 12 na rikici
  • Ya ce, akalla kashi 10 na mutanen jihar sun watse kuma har yanzu ba a san inda suke ba
  • Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja

Abuja - Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana cewa ba a san inda akalla 10% cikin 100% na al'ummar jihar suke ba sakamakon rikicin 'yan ta'adda a jihar, The Nation ta ruwaito.

Zulum, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar gwamnati bayan wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, ya kuma ce an kashe mutane sama da 100,000 a cikin shekaru 12 da suka gabata na rikicin Boko Haram.

Kara karanta wannan

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Gwamnan, wanda ya ce ya tattauna rahoton mika wuya da mayakan Boko Haram suka yi da Shugaban kasa, ya kara da cewa bai ga dalilin da zai sa a ki amincewa da wadanda suka mika wuya ba.

Da dumi-dumi: Kashi 10 na jama'ar Borno sun bace saboda Boko Haram, inji Zulum
Labari da dumi-dumi daga Legit.ng Hausa | Hoto: legit.ng
Asali: Original

Zulum ya kuma ce akwai jimillar 'yan ta'adda 2,600 da suka mika wuya a yanzu da ake tsare da su, inda ya jaddada cewa ba dukkan su ba ne masu laifi.

Ya ce daga cikin wadanda suka mika wuya akwai wadanda ba su ji ba ba su gani ba da aka tilasta masu shiga kungiyar ta Boko Haram yayin da wasu kuwa yara ne matasa ne da basu kai tantance mai kyau ba.

Yayin da yake bayyana cikakken goyon bayansa ga 'yan ta'addan da suka mika wuya, ya ce gwamnatin Borno ba ta tunanin ba wa 'yan ta'adda da suka tuba wani gata don sun mika wuya.

Kara karanta wannan

Abin da yasa ba za mu hukunta tubabbun ƴan Boko Haram ba, Gwamnatin Tarayya

Gwamnan, wanda ya ce maharan sun kai masa hari kusan sau 50, ya kuma yi alkawarin tallafa wa wadanda harin ya rutsa da su.

Ya kamata a kula, watakila tuban muzuru 'yan Boko Haram ke yi, in ji Ahmed Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce dole ne ‘yan Najeriya su yi taka tsantsan wajen karbar 'yan Boko Haram da ke ikirarin sun mika wuya kuma suna neman gafara, in ji rahoton The Cable.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a ranar Litinin 23 ga watan Agusta, Lawan ya ce dole ne a samar da matakan da za su tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun yi tuban gaskiya.

Hedkwatar Tsaro (DHQ) ta ce sama da 'yan ta'adda 1,000, ciki har da kwamandojin Boko Haram da kwararrun sarrafa bama-bamai sun mika wuya ga sojojin rundunar Operation Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Auren dan Shugaba Buhari: Talakan Najeriya ya shiga uku – In ji Sheikh Ahmad Gumi

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon da mutum 50, sun hallaka mutum 4 a Maradun

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Litinin 23 ga watan Agusta ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka mutum hudu tare da yin awon gaba da wasu mutum 50 a garin Goran Namaye da ke karamar hukumar Maradun.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, Muhammad Shehu, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Muhammad Shehu, ya ce maharan, wadanda suka zo da yawansu, sun mamaye garin da tsakar daren ranar Lahadi, inda suka kashe mutum hudu tare da sace wasu 50.

Asali: Legit.ng

Online view pixel