Ku Tuba Ku Miƙo Makamanku, Ko Ku Fuskanci Ƙalubale, Sabon Kwamishinan Ƴan Sandan Zamfara
- Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Yakubu Elkana, ya ja kunnen ‘yan bindiga
- CP Elkana ya ce ko dai su zubar da makamansu ko kuma su yabawa aya zakinta a jihar
- Ya yi wannan furucin ne a Gusau ranar Laraba, yayin tattaunawa da manema labarai
Zamfara - Sabon kwamishinan jihar Zamfara, Yakubu Elkana, ya ja kunnen shu’uman ‘yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara inda yace ko dai su zubar da makamansu ko kuma su fuskanci hukunci mai muni.
Kamar yadda Channels TV ta wallafa, Elkana ya yi wannan furucin ne yayin tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Laraba, inda ya hori ‘yan bindiga suyi gaggawar baiwa gwamnatin jihar hadin kai wurin samar da zaman lafiya ko kuma su ga aiki da cikawa.
Abinda sabon kwamishina ya sanar da 'yan bindiga
Tsarin aikina cikin dabara zai fara, zamu yi amfani da salo na musamman wurin bi daki-daki don kawo karshen rashin tsaro a fadin jihar nan.
Zamu zabura wurin mayar da hankali akan yaki da duk wasu ‘yan ta’adda da masu taimaka musu su fuskanci hukunci daidai da laifinsu ta hanyar amfani da jama’an gari wurin cimma wannan kudiri namu.
Jajircewarmu da mayar da hankalinmu a matsayin jami’an ‘yan sanda zai taimaka mana wurin gaggawar kawo karshen ta’addanci a jihar nan, sannan zamu yi amfani da tsare-tsaren da sifeta janar na ‘yan sanda ya samar da kuma hanyar samar da zaman lafiya da gwamna Bello Matawalle ya kirkiro.
Wannan shine abinda na mayar da duk hankalina akai a matsayina na kwamishinan ‘yan sandar jiharnan,” a cewar Elkana.
Yakubu Elkana ya roki jama'ar jihar alfarma
Sannan kwamishinan ya kara da rokon jama’an gari da su yi kokarin baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai wurin dakatar da duk wasu ta’addanci a fadin jihar.
A karkashin mulkina, ‘yan sanda zasu yi kokarin ganin sun yi amfani da kwarewa irin tamu don shawo kan kowacce irin matsala.
Zamu bi wasu hanyoyin don dakatar da ta’addanci, shiga hakkin bil’adama, rashawa da sauran miyagun ayyuka a fadin jiharnan,” a cewarsa.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, kwamishinan ya yabawa ‘yan jarida akan yadda suke baiwa ‘ya nsanda hadin kai don tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Yan jarida suna kokari kwarai kuma mutanen kirki ne. Don yabon ku bata baki ne.
Don haka ina mika godiyata gareku akan hadin kan da kuke baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro,” a cewar Elkana.
'Yan Bindiga Sun Afka Gidajen Mutane Da Tsakar Dare, Sun Sace Manya Da Yara a Niger
A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kai hari garin Kwankwashe da ke kan hanyar Suleja zuwa Madalla, a jihar Niger a safiyar ranar Laraba sun sace mutane ciki har da yara, Daily Trust ta ruwaito.
Wani shaidan gani da ido ya ce an sace mutane daga gidaje uku da kuma wani otel da ke Unguwar Fulani a yankin.
Wata yar unguwar, Faith Lucky, wacce aka sace yaranta biyu, yarinya mai shekara 17 da yaro mai shekara 15, ta ce ta gane cewa sun iso gidanta ne yayin da suka fara buga kofar shiga gidan.
Asali: Legit.ng