Adam Zango ya bayyana abu ɗaya da ya ke jira ya samu kafin ya dena yin fim kwata-kwata

Adam Zango ya bayyana abu ɗaya da ya ke jira ya samu kafin ya dena yin fim kwata-kwata

  • Jarumi Adam Zango ya ce jira kawai ya ke yi ya samu wata sabuwar hanyar samun kudi sannan ya dena fim
  • Zango ya bayyana hakan ne cikin wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar 21 ga watan Agusta
  • Adam Zango ya ce yana yi wa Allah godiya bisa daukakan da ya samu da fim amma yanzu bai cika sha'awar yin fim ba

Jarumin Kannyood, Adam Zango ya ce akwai yiwuwar ya dena yin fim a masana'antar fim na Hausa idan ya samu wata sabuwar hanyar samun kudaden shiga, Premium Times ta ruwaito.

Jarumin ya ce a sha'awar da ya ke yi wa masana'antar na fim ta ragu duk da cewa har yanzu yana cikinta. Ya ce idan ya samu hanyar samun kudaden shiga da ta fi fim, zai dena yin fim.

Kara karanta wannan

Auren dan Shugaba Buhari: Talakan Najeriya ya shiga uku – In ji Sheikh Ahmad Gumi

Adam Zango ya bayyana abu ɗaya da ya ke jira ya samu kafin ya dena yin fim kwata-kwata
Jarumi Adam Zango: Hoto: Naira Gent
Asali: Facebook

A cikin hirar da aka yi da shi a BBC Hausa a ranar Asabar, Zango ya ce:

"Ni fitaccen jarumi ne a Kannywood kuma ina yi wa Allah godiya bisa wannan baiwar, amma duk da haka ina da shirin neman wata hanyar samun kudi da ta fi wannan, zan dena fim din inyi wani abu daban da zarar na samu."

Zango ya kuma bada dalilin abin da yasa bai cika son fita kasashen waje ba kamar sauran takwarorinsa, yana mai cewa:

"Bana son jirgin sama, bana kaunar jirgi don haka na ke kokarin ganin babu wata dalilin da zai sa in shiga jirgin. Tafiya da na yi mafi tsawo shine zuwa Landan a 2016."

Zanga ya taba barazanar barin Kannywood a baya

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

A watan Satumban 2019, jarumin ya taba sanar da cewa ya fita daga Kannywood.

A wani faifan bidiyo na minti tara da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Zango ya ce takwarorinsa na yi masa hassada saboda nasarorin da ya ke samu.

Ya ce:

"Takwarori na a Kannywood ba su tare da ni a yanzu. Ba su kauna ta kuma suna hassada bisa nasarar da na ke samu. Suna dauka na kamar sabon shiga kuma ba su dauka na da muhimmanci. Don kawai Allah ya daukaka ni kuma na fi su cigaba.
"Kimanin kashi 90 cikin 100 na manyan yan Kannywood na min hassada. Sun ki jini na. Don kawai na fi su samun nasara. Suna daukan nauyin mutane su rika suka na a kafafen sada zumunta don kawai na fi su.
"Na gaji da hakan shi yasa na fice daga Kannywood na tsaya tare da tsiraru da ke tare da ni."

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Tuni dai jarumin ya kafa sabuwar masana'antar fim a Kaduna mai suna Kaddywood.

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.

Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164