Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalai da suka tasku dalilin ambaliyar ruwan sama
  • Shugaban ya ce, gwamnati za ta duba mai yiwuwa wajen taimaka musu ta wasu hanyoyinta
  • Hakazalika ya bukaci mutane da su rika kula da gargadin da ake yi game da hasashen yanayi

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna juyayi ga iyalai da sauran wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su sakamakon ci gaba da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a makwannin da suka gabata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan lamarin da ya shafi dubban mutane a jahohi 32 na Najeriya, ya haifar da asarar gidaje, gonaki, rayuka da rushewar rayuwa ta yau da kullun.

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wabarna, ya ce zai taimaka musu
Shugaba Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban, wanda ya koma aiki a ranar Laraba bayan kebewa na kwanaki biyar bayan balaguro zuwa Landan, ya nuna damuwa kan halin da ake ciki, in ji News Diary.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyoyin shagalin saka lallen auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Abuja ya nakalto shugaban yana cewa:

"A ko yaushe ina sa ido kan lamarin kuma za mu tabbatar da duk wani taimako da za a iya bai wa wadanda abin ya shafa."

Ya kamata a habaka al'adar girmama lamarin hasashen yanayi

Shugaba Buhari, duk da haka, ya yi kira da a sami kyakkyawan hadin kai tsakanin hukumomin tarayya ciki har da hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa da gwamnatocin jihohi don habaka al'adar girmama hasashen yanayi.

Ya ci gaba da cewa dole ne 'yan kasa su yi aiki da gargadin farko na yanayi don kaucewa afkuwar bala'i a kowace shekara.

Shugaban ya yarda cewa wasu jihohi sun dauki gargadin da aka fada a lokuta daban-daban game da ambaliyar ruwa, inda ya ambaci takamaiman yankuna da al'ummomin da NEMA ta ambato, amma wasu yankuna sun yi biris da gargadin.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Ya kuma yabawa jihohi kalilan da suka dauki mataki mayar da martani bayan gargadin kuma kwalliya ta biya kudin sabulu wajen gujewa barnar da asarar da ke faruwa.

Shugaban ya amince da taron bitar da NEMA za ta yi a cikin makonni masu zuwa wanda zai tara dukkan hukumomin bayar da agajin gaggawa na jihohi daban-daban.

Hayakin janareto ya hallaka mutane 7 'yan gida daya a jihar Osun

A wani labarin, An tsinci gawar wasu mutane bakwai 'yan gida daya a cikin dakunansu a karamar hukumar Apomu ta jihar Osun, ranar Talata 17 ga watan Agusta.

Rundunar 'yan sandan Osun ta ce ana zargin hayaki daga janareto ne sanadin mutuwarsu, amma sakamakon binciken gawa zai tabbatar da musabbabin mutuwar tasu.

Yemisi Opalola, mai magana da yawun rundunar, ta ce akwai mutane takwas a dakuna daban-daban na gidan amma mutum daya ne kawai aka tarar yana numfashi.

Kara karanta wannan

Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel