A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

  • An bayyana cewa mafarauta a yankin arewacin Najeriya sune ainihin wadanda masu tada kayar baya ke tsoro
  • Kungiyar ta Arewa Consultative Forum (ACF) wacce ta goyi bayan kiran da Gwamna Bello Masari yayi na kare kai ga mutanen Katsina ce ta bayyana haka
  • Kungiyar ta yi ikirarin cewa mafarautan na fin karfin 'yan ta'addan kusan a koda yaushe saboda sun fi fahimtar yankin

Kira ga kare kai da Gwamna Bello Masari yayi wa mazauna Katsina ya samu goyon baya daga wasu kungiyoyin al'adu na arewacin kasar, wanda daya daga cikinsu ita ce Arewa Consultative Forum (ACF).

Kungiyar ta ce Masari ya yi daidai da ya roki mutanensa da su dauki makamai don yaki da 'yan fashi da masu garkuwa da mutane, ta kara da cewa ba dukkan makamai ne suka zama haramun ga yan kasa ba, musamman wadanda ke zuwa da izinin 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Kara yawa da al'ummar Afrika ke yi na hana ni bacci cikin dare

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoron fiye da 'yan sanda da sojoji
Kungiyar Arewa ta ce Boko Haram ba tsoron mafarauta fiye da 'yan sanda da sojoji Hoto: Governor Aminu Bello Masari
Asali: Facebook

Sakataren yada labarai na ACF na kasa, Emmanuel Yawe, wanda ya zanta da jaridar Punch a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, ya bayar da hujjar cewa mafarautan suna cikin wadanda aka ba damar daukar bindiga.

Da yake karin haske, Yawe ya yi bayanin cewa misalai da yawa sun tabbatar da cewa 'yan ta'adda a arewa suna tsoron wadannan mafarautan har ma fiye da hukumomin tsaro na yau da kullun kamar 'yan sanda da sojoji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Kar ku manta cewa mafarauta a Adamawa sun sawa Boko Haram zafi. Boko Haram sun tsorata da su fiye da rundunar sojoji da 'yan sanda.
“Mutanen yankin sun san filin fiye da sojoji da ‘yan sanda, waɗanda aka tara su daga ko'ina cikin ƙasar bisa tsarin Gwamnatin Tarayya kan ɗaukar ma’aikata a hukumomin gwamnati. Ba mamaki an tattara su (mafarauta) don shiga yaƙi da Boko Haram."

Kara karanta wannan

Har yanzu bamu kammala bincike kan Abba Kyari ba, Hukumar yan sanda

Gwamnan Katsina: Ku ma ku sayi bindiga ku kare kanku daga 'yan bindiga

A baya mun kawo cewa Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yi kira ga mutanen da ke zaune a yankunan da ke da yawan 'yan bindiga da su mallaki makamai su kare kansu daga ta'addanci.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na yada labarai ga gwamnan, Abdu Labaran Malumfashi ya fitar, wanda Daily Trust ta samu.

Gwamnan ya ce ba daidai ba ne mutane su mika wuya ga 'yan bindiga ba tare da wani yunkuri na kare kansu ba, lura da cewa tsaro aikin kowa ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel