Auren dan Shugaba Buhari: Talakan Najeriya ya shiga uku – In ji Sheikh Ahmad Gumi

Auren dan Shugaba Buhari: Talakan Najeriya ya shiga uku – In ji Sheikh Ahmad Gumi

  • Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani a kan daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf
  • Gumi ya yi tir da yadda manyan jami'an gwamnati suka kashe dukiya domin halartan wannan biki a jihar Kano
  • Ya kuma bayyana cewa talakan Najeriya ya shiga uku sai dai ya koma ga Allah domin samun ceto

Kano - Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya yi raddi a kan bikin dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, Zahra.

Malamin ya yi watsi da yadda jami'an gwamnati suka kashe kudi domin halartan wannan biki a jihar Kano, inda ya bayyana hakan a matsayin almubazaranci da dukiyar kasa.

Auren dan Shugaba Buhari: Talakan Najeriya ya shiga uku – In ji Sheikh Ahmad Gumi
Sheikh Gumi ya shawarci talaka da ya koma ga Allah Hoto: Punchng.com/Daily Trust
Asali: UGC

Gumi a cikin wani bidiyo da aka wallafa a dandalin Sunnah ya kuma bayyana cewa talakan kasar nan ya shiga uku sai dai ceton Allah kawai, sannan ya shawarci talakawa da su koma ga Allah da gaskiya domin ya cece su.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Ya yi misali da yadda jirage masu zaman kansu suka cika jihar Kano da sunan auran dan shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Mutane suna tsammanin idan an baka shugabanci ba za a yi maka hisabi da misalai ba, toh za a yi maka. Umar Bin Khatab shine Khalifa wata rana yayi huduba ya ga sadaki yana tsada, yace inda makaruma ce da kuma taqawa daga Allah Annabi ya fi kowa cancanta idan yayi aure ko ya aurar da ‘yayan shi a samu sadaki yayi yawa. Sai yace amma dukka auran da yayi ko ya aurar bai taba wuce haukiha 12 ba wanda yayi daidai da N400,000 na yanzu.
"Wani ya fada mun a Abuja cewa da kudinka babu jirgi mai zaman kansa da zai kai ka Kano, duk wadanda suke nan an siye su sun yi Kano saboda Shugaban kasa zai aurar da dansa. A halin da ake ciki, ga mutane chan tsattsare wani tsare a daji wani tsare a cikin gari.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaba Buhari zai gana da shugabannin tsaro

"Ga yunwa, duk matsalar da ka sani akwai ta. Sannan abun da kuka je ba ibada bane wa yace ku je? Annabi SAW ya aurar da diyarshi wa ya kira? Ace annabi zai yi aure mutanen Makkah, mutanen Yemen su zo annabi zai auri mace ace ku zo? Ace duk Madina babu adilai da za su shaida cewa annabi yayi aure? Wa yace ku zo? Da kudin mutane.
"Na biyu dukiyar mutane, sannan mutanen nan da suna cikin wadata ne, toh basa cikin wadata suna cikin wahala, duk irin wahalar da ka sani a cikin kasar nan akwai ta. Ina ku ina irin wannan almubazaranci a cikin kasa.
"Sannan kai shi talakan Najeriya ya shiga uku, Allah ya shiga uku, ya koma ga Allah kawai, talaka ya koma ma Allah da gaske sai Allah ya cece shi. Allah kadai zai iya ceton talaka, amma ya koma ma Allah ba da yaudara ba, idan bah aka ba irin wannan abun bai kamata ba a cikin irin wannan zamani.

Kara karanta wannan

'Bani da burin zama shugaban kasa': Tsohon sarkin Kano Sanusi ya yi watsi da siyasa

"Kuna ganin Sardauna zai iya yin haka? Toh me yasa muka lalace haka? Mun dauki mulkin nan kuma zuwa yake yi kamar hadari ne ya zo ya wuce. Mulki na Allah ne, idan kana mulki ka ji tsoro kujerar Allah ce ya dan baka ka dandana."

An daura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero kan sadaki N500,000

A baya mun kawo cewa Allah ya yadda, alkawari kuma ya cika. An daura auren Yusuf Muhammadu Buhari, da daya tilo namiji na shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero, diyar mai martaba Sarki Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero.

Babu shakka garin Bichi dake jihar Kano ya cika dankam da jiga-jigai na fadin kasar nan har da kasashen ketare, wadanda suka dinga tururuwar zuwa shaida daurin auren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel