Abun da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano wacce ta sace zuciyar da namiji daya tilo da Buhari ya mallaka
- Zahra Nasiru Bayero ita ce matashiyar da ta sace zuciyar ‘da namiji daya tilo da Buhari ya mallaka
- Ta kasance 'ya ta biyu a wajen Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero
- Matashiyar na karantar fannin gine-gine a wata jami'a a kasar Ingila
A cikin 'yan sa'o'i kadan daga yanzu, Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari daya tilo, zai angwance da Zahra, diyar Alhaji Nasir Ado Bayero, Sarkin Bichi.
Tuni Kano ta fara cika kuma jami'an tsaro sun mamaye wurare masu mahimmanci a cikin garin.
Anan akwai abubuwan ban sha'awa da yakamata ku sani game da surukar shugaban kasar ''mai shigowa'':
'Yar Sarkin Bichi
Zarah Ado Bayero 'ya ce ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero mai shekara 20, wanda shi ne na hudu a ‘ya’yan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
Baya ga kasancewarsa Sarki, mahaifinta shi ne kuma shugaban kamfanin 9mobile. Shi ne ɗan fari da aka haifa a gidan masarautar Kano da ake kira Gidan Dabo.
Ya kasance hakimin kananan hukumomin Fagge, Tarauni da Nassarawa kafin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta nada shi a matsayin sarki mai daraja na daya.
Nasabarta da Sokoto
Yayin da mahaifiyar Zarah, Farida Imam, ta kasance diyar shahararren masanin ilimi na Kano, Mal Abubakar Imam (Imamu Galandanci), tsohon Babban Darakta a Afribank Plc, Sarkin Musulmi, Muhammad Saad Abubakar III, yana auran ‘yar uwar Farida, Daily Trust ta ruwaito.
Ilimi
Zarah, ita ce 'yar sarki ta biyu kuma ta karanci fannin gine -gine a Ingila.
Sarauta ta hadu da mulki, za a daura auren Yusuf Buhari da Gimbiyar Kano a yau
A gefe guda, an tsananta tsaro a duk wasu hanyoyi da za su kai garin Bichi, inda masarautar sarkin Bichi take, Alhaji Nasir Ado Bayero, sakamakon daurin auren diyarsa Zahra, da dan shugaban kasa Muhammadu Buhari daya tal, Yusuf da za a daura yau a masarautar.
Daurin auren shine batun da ake magana akai tun watanni da dama da suka gabata a kafafen sada zumuntar zamani kuma cece-kuce iri-iri sun yawaita inda ake cewa biki ne na shugabannin kasa da masu sarauta.
Ana sa ran shugaba Buhari wanda bai dade da dawowa daga wata tafiyar aiki da neman lafiya ba ya halarci daurin auren dan nasa kamar yadda kwamitin tsare-tsare wacce masarautar Bichi ta kafa ta shirya.
Asali: Legit.ng