Hotunan Fani-Kayode yayin da ya shiga sahun manyan ‘yan APC don halartan daurin auren dan Buhari
- Femi Fani-Kayode ya bi sahun manyan 'yan APC don halartan daurin auren dan Shugaban kasa, Yusuf Buhari a jihar Kano
- Fani Kayode ya kasance babban mai sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Za a kulla aure tsakanin Yusuf da Zahra Bayero a yau Juma’a, 20 ga watan Agusta
Bichi, jihar Kano - Femi Fani-Kayode, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, ya shiga cikin wasu manyan jiga-jigan ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin daurin auren dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Mun kawo a baya cewa dan Shugaba Buhari daya tilo, Yusuf zai auri diyar Alhaji Nasir Ado Bayero, Sarkin Bichi a yau Juma’a, 20 ga watan Agusta.
Garin ya riga ya cika ya tumbatsa sannan kuma jami'an tsaro sun mamaye manyan wurare a duk faɗin Kano.
A wasu hotuna da ya wallafa a kafafen sada zumunta, an ga Fani-Kayode, babban mai sukar gwamnatin Buhari, tare da wasu manyan ‘yan APC.
Wasu daga cikin gwamnonin da aka gani da FFK sune Babagana Zulum (Borno) da Bello Matawalle (Zamfara).
Isa Pantami, Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, shi ma ya ɗauki Hoto tare da Fani-Kayode.
Ya wallafa a shafinsa na Instagram:
“Na dira Kano tare da abokaina da 'yan uwana Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, Gwamna Babagana Umar Zulum na jihar Borno, Sanata Sani Ahmed Yarima, Sanata Ali Ndume, Ambasada Bashir Yuguda, Hon. Minista Isa Pantami, Mallam Nuhu Ribadu da sauran su domin daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, da diyar Sarkin Bichi, HRH Nasiru Ado Bayero, Zahra Ado Bayero. ”
Abun da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano wacce ta sace zuciyar ‘da namiji daya tilo da Buhari ya mallaka
Daurin auren Yusuf Buhari: Yemi Osinbajo ya dira garin Kano
A gefe guda, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya isa filin jirgin sama na Aminu Kano da ke jihar Kano domin daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ne ya tarbi mataimakin shugaban kasar.
Shugabannin biyu tare da wasu manyan jami'an gwamnati suna jiran shugaban kasa, wanda ake sa ran zai tashi daga Yola, babban birnin jihar Adamawa, kowane lokaci daga yanzu.
Asali: Legit.ng