Buhari ya sha alwashin kara kasafin ilimi da kashi 50% a cikin shekaru 2
- Shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka alkawarin karin kasafin ilimi da kashi hamsin
- Ya sanar da hakan ne a wata takarda da yasa hannu a babban taron habaka ilimi da ya hallarta a kasar Ingila
- Shugaban yace zai bada damar ilimi ga kowanne dan kasa tare da bada matukar fifiko ga ilimantar da yara mata
London, Ingila - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin karin kasafin bangaren ilimi da kashi hamsin a cikin shekaru biyu masu zuwa, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Shugaban kasan ya sha wannan alwashin ne a wata takarda da ya saka hannu a gagarumin taron ilimi na duniya da yake halarta a yanzu haka a birnin London dake Ingila.
KU KARANTA: El-Rufai ya sanar da abinda suke yi da gwamnatin Nasarawa wurin ceto basaraken jiharsa
KU KARANTA: EFCC ta daskarar da asusun bankin 'yar majalisa bayan ta siya motar N1bn
Mun mayar da hankali wurin karin kasafin kudi a fannin ilimi na kowacce shekara da kashi 50% a shekaru 2 masu zuwa kuma zamu kai 100% zuwa 2025," Shugaban kasan yace.
Daily Trust ta ruwaito cewa taron ya samu shugabancin firayim ministan UK Boris Johnson da shugaban kasan Kenya Uhuru Kenyatta domin bada dama ga shugabanni wurin dauka alkawarin tallafawa fannin ilimi a kasashe casa'in.
A alkawarin da Buhari yayi a ranar Laraba kamar yadda mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya sanar, ya ce zai tabbatar da cewa dukkan 'yan kasa sun samu ilimi tare da jaddada na fannin yara mata.
Gwamna Matawalle ya bayyana abinda ke assasa ta'addanci
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya alakanta cigaban miyagun lamurran 'yan bindiga da kuma garkuwa da mutane da ake yi a jihar da rikicin makiyaya da manoma na baya.
Matawalle ya kara da cewa rashin shiga sasancin wasu jihohin arewa maso yamma da 'yan bindiga yana daga cikin dalilan dake cigaba da assasa rikici, Channels TV ta ruwaito.
Har ila yau, gwamnan wanda yace kashe fitattun shugabannin Fulani na Dansadau suna daga cikin abubuwan dake kara rura wutar ta'addanci a jihar.
Ya kara da cewa mabiyan shugabannin Fulanin Zamfara, Kebbi da Sokoto ne suka fusata kuma suke kai farmaki kan wadanda suke zargin sun kashe shugabannninsu.
Asali: Legit.ng