Tsadar abinci: Dalilin da yasa 'yan Najeriya za su ci gaba da cin bakar wahala, in ji masana
- Binciken masana ya bayyana dalilin da yasa 'yan Najeriya za su ci gaba da shan wahala
- Binciken ya nuna cewa, ba lallai a cimma burin sauke farashin kaya a nan da shekarar 2022 ba
- Wannan batu na masana ya biyo bayan hasashen CBN cewa, nan da 2022 komai zai daidaita
Najeriya - Masana tattalin arziki a Najeriya na gargadin cewa zai yi matukar wuya a iya cimma hasashen nan da babban bankin kasar CBN ya yi na sa ran saukar farashin kayayyaki.
Babban bankin ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2022, farashin kayan abinci zai sauka da 10% cikin 100%, saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da kuma rashin bin matakan da suka kamata.
Kasimu Garba Kurfi, wani masanin tattalin arziki da ke birnin Legas, yana cikin masu irin wannan ra'ayi.
Legit Hausa ta gano cewa, ya shaida wa BBC cewa matukar mahukunta ba su tashi tsaye wajen daukar matakin da ya kamata ba, lamarin zai ci gaba da lalacewa ne maimakon ya gyaru.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"Abu ne mai wuya a iya samun wani cigaba, saboda halin da muka samu kanmu, ga rashin aikin yi, ga matsalar tsaro an kasa magance ta, don haka dukkan wadannan matsaloli akwaisu, kuma baza su bada damar haifar da wani sauyi ba."
Da yake ba da shawara kan mafita, ya kara da cewa:
"Abun da gwamnati ya kamata ta yi shi ne ta fadada hanyoyin samun kudi, domin ta iya aiwatar da manufofinta na yau da kullum, sannan a samar da zaman lafiya don in akwai shi to mutane za su iya fita su nemi na kansu".
Tsadar Abinci: CBN Ta Kawo Mafita, Za Ta Karya Farashin Shinkafa a Najeriya
A baya cikin watan Yuni, a kokarinsu na samar da wadataccen abinci ga 'yan Najeriya tare da karya farashin shinkafa, CBN da Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya, sun fara batun kaddamar da sayar da tan miliyan tara na tallafin shinkafa ga masu sarrafata.
Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele yayin da yake kaddamar da shirin sayarwar da kuma fara noman rani a Kaduna ya ce, bankin a shirye yake ko yaushe don tallafawa harkar noma, The Nation ta ruwaito.
Ahmed Mohammed na CBN reshen jihar wanda ya wakilci gwamnan, ya ce shirin an shirya shi ne don sayar da shinkafar a kan farashi mai rahusa da nufin karya farashin don amfanin kowa a Najeriya da ma wasu kasashen.
Gwamnan Babban Bankin ya ce, bankin a shirye yake domin tabbatar da wadatar abinci da inganta noman shinkafa a kasar.
A cewarsa:
"Wannan shirin shiri ne na kasa baki daya da nufin samar da abinci ga kowa, shi ya sa Babban Bankin a ko yaushe a shirye yake ya tabbatar akwai kudade ga manoma."
Wakilin Daraktan Habaka Kudi na Babban Bankin, Mista Chika Nwaja, ya ce Bankin na da aniyar cire batun ‘yan tsakiya daga sayar da shinkafa ga masu sarrafawa don 'yan Najeriya su saya a farashi mai rahusa.
A nasa jawabin, Shugaban kungiyar Manoman Shinkafa ta kasa (RIFAN), Alhaji Aminu Goronyo, ya ce duk abin da ke faruwa a wurin taron shi ne Babban Bankin wanda ya amince da hakan don kawai ciyar da kasar nan gaba.
Yaya batun tsadar abinci?
A baya, Bankin Duniya ya fitar da rahoton cewa sama da mutane miliyan bakwai sun sake fadawa talauci a bara saboda karuwar hauhawar farashi a Najeriya.
Hakazalika ya ce a cikin watan Afrilun da ya wuce an samu hauhawar farashi mafi yawan da ba a taba gani ba a cikin shekara hudu.
Rundunar sojin Najeriya ta yi martani yayin da matar marigayin kanal ta yi ikirarin cewa kashe mijinta aka yi
Rahoton na Bankin Duniyar ya yi ishara da abin da ya kira da fitattun kwaskwarima na gwamnati.
A cewarsa, wannan na nufin shawo kan tasirin anobar cutar korona da kuma tallafawa wajen farfado da tattalin arziki, ciki har da matakan rage tallafin man fetur, da daidata farashin wutar lantarki.
Dukkansu kuma in ji rahoton don bunkasa kafofin samun kudin shiga da nufin aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar talaka ne
Tsadar abinci: Ba fa zai yiwu mu yi kasa da farashin buhun shinkafa ba inji ‘Yan kasuwa
A wani labarin daban, Kungitar RIPAN ta masu aikin gyara shinkafa a Najeriya, ta reshen jihar Kano ta yi bayanin abin da ya sabbaba tashin farashin da ake fuskanta a yau.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto inda aka ji wani daga cikin ‘ya ‘yan wannan kungiya ya na karin-haske a kan abin da ya sa buhu ya kai N23, 000.
Alhaji Abba Dantata a madadin kungiyar RIPAN, ya zanta da ‘yan jarida tare da hukumar PCACC ta jihar Kano, bayan wani zama da su ka yi a makon nan.
Asali: Legit.ng