Akwai Babbar Matsala, Zulum Ya Bayyana Halin da Borno Ta Shiga Saboda Mika Wuyan Yan Boko Haram

Akwai Babbar Matsala, Zulum Ya Bayyana Halin da Borno Ta Shiga Saboda Mika Wuyan Yan Boko Haram

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Zulum, yace jiharsa na cikin tsaka mai wuya bayan mika wuyan yan Boko Haram
  • Zulum yace ba abune mai sauki mutum ya iya amincewa da wanda ya kashe masoyinsa ba kuma ya rayu tare da shi
  • Gwamnan yace zai gana da shugaba Buhari da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo mafita

Borno - Gwamnan Borno, Babagana Zulum, yace jihar Borno ta shiga wani mawuyacin hali saboda mika wuyan da mayakan Boko Haram ke yi.

Gwamnan yace lamarin yana bukatar kulawa daga masu ruwa da tsaki da wakilan yankunan da lamarin ya shafa domin su haɗa kai a nemi hanyar warware damuwar.

Zulum ya faɗi hakan yayin ziyarar da yakai garuruwan Bama da Gwoza ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Wannan Shiryayyen Kisa Ne, Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai da Kisan Musulmai a Jos

Wannan na kunshe ne a cikin wani rubutu da gwamna Zulum ya yi a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook.

Gwamna Zulum Tare da Sojoji
Akwai Babbar Matsala, Zulum Ya Bayyana Halin da Borno Ta Shiga Saboda Mika Wuyan Yan Boko Haram Hoto: Gwamnan Borno FB Fage
Asali: Facebook

Me yakai Zulum Bama da Gwoza?

Gwamna Zulum yakai ziyara waɗannan garuruwa ne domin aikin jin kai da kuma duba cigaban da aka samu.

Kafin daga bisani ya yi jawabi ga jami'an sojojin Bama da Gwoza, shugabannin yanki a fadar sarkin Gwoza da Shehun Bama.

Gwamna Zulum ya yi jawabi iri ɗaya a dukkan garuwawan biyu, inda yace:

"Mu a jihar Borno muna cikin mawuyacin hali, dole ne mu zaɓi ɗaya cikin abu biyu masu wahala, kodai mu zaɓi yaƙi da yaki ci yaki cinyewa ko kuma mu amince da yan ta'adda dake mika wuya suna son dawowa cikinmu."
"Abu ne mai matukar wuya garemu musamman waɗanda suka rasa yan uwansu da sojojin da suka rasa abokan su, su iya rungumar waɗannan tubabbun mayakan har mu rayu tare da su."

Kara karanta wannan

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

"Babu wanda zai iya cigaba da rayuwa da wanda ya kashe mahaifansa ko wasu yan uwansa, masoyansa kuma a wuri ɗaya."

Ina babbar matsalar take?

Gwamnan yace amincewa da yan Boko Haram yana tattare da hatsarin bata wa wasu rai, waɗanda aka kashe yan uwansu, kuma suna iya yin bore.

A ɗaya bangaren kuma, Zulum yace kin Amincewa da su ka iya sanya su jone da mayakan ISWAP su kara musu karfi.

Gwamnan ya bayyana cewa zai tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari da manyan hafoshin tsaro da shugabannin al'umma da malaman addini.

Hakanan yace zai tatattuna da ƴan majalisar wakilai da malaman makaranta da sauran masu ruwa da tsaki musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa don ganin an samo mafita a wannan lamari.

A wani labarin kuma Kisan Gillan Musulmi a Jos: Kungiyar Kare Hakkin Musulmai MURIC Ta Yi Kira a Kame Kiristocin Irigwe baki ɗaya

Kara karanta wannan

Abun Farin Ciki: Gwamna Zulum Ya Jagoranci Sanya Marayu 5,361 Makaranta a Monguno

MURIC ta yi kira ga gwamnati ta kame baki ɗaya kiristocin Irigwe domin suna da hannu a kisan gillan musulmai a Jos.

Ƙungiyar mai fafutukar kare hakkin musulmai tace hankali ba zai ɗauki maganar da gwamnan Ondo ya yi ba.

Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a shekarar 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya yi karanci Lissafi a digirinsa na farko a jami'ar kimiyya da fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags:
Online view pixel