Kisan Gillan Musulmi a Jos: Kungiyar Kare Hakkin Musulmai MURIC Ta Yi Kira a Kame Kiristocin Irigwe

Kisan Gillan Musulmi a Jos: Kungiyar Kare Hakkin Musulmai MURIC Ta Yi Kira a Kame Kiristocin Irigwe

  • MURIC ta yi kira ga gwamnati ta kame baki ɗaya kiristocin Irigwe domin suna da hannu a kisan gillan musulmai a Jos
  • Ƙungiyar mai fafutukar kare hakkin musulmai tace hankali ba zai ɗauki maganar da gwamnan Ondo ya yi ba
  • MURIC ta kuma bukaci a yiwa musulman Najeriya bayani kan inda aka kwana a binciken kisan Janar Alkali

Plateau - Kungiyar fafutukar kare hakkin musulmai (MURIC) ta yi kira da a gaggauta kame gaba ɗaya waɗanda suka aikata kisan musulmai matafiya a Jos, inda ta kira su da "Mayakan kiristoci a Jos."

Daily Nigerian ta ruwaito cewa matafiya musulmai 25 wasu sojojin ƙungiyar kiristanci suka kashe a Rukaba, jihar Filato ranar Asabar.

A wani jawabi da daraktan MURIC, Ishaq Akintola, ya fitar, ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa musulmai, tare da kira ga gwamnati ta kame waɗanda suka aikata kisan.

Shugaban MURIC da Shugaba Buhari
Kisan Gillan Musulmi a Jos: Kungiyar Kare Hakkin Musulmai MURIC Ta Yi Kira a Kame Kiristocin Irigwe Hoto: kemifilani.ng
Asali: UGC

Wani sashin jawabin yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Matafiyan sun halarci taron zikiri na shekara-shekara a Bauchi, kuma suna kan hanyar komawa Ikare, jihar Ondo yayin da sanannun sojojin kungiyar kirictoci ta Irigwe suka tare su."
"Musulman a cikin tawagar motocin Bas guda biyar babu makamai a tare da su, an tilasta musu fitowa sannan aka kashe su ɗaya bayan ɗaya. Sun kashe mutum 22 sannan suka jikkata 14."
"Karisowar jami'an tsaron yan sanda da sojoji shine ya ceci ragowar mutanen."

Shin mutum 6 ne kaɗai suka aikata kisan?

Farfesa Ishaq Akintola, ya cigaba da cewa:

"MURIC ta yi Allah wadai da wannan kisan gillan da karfin murya, kuma muna bukatar a zagaye sojojin Irigwe a kame su baki ɗaya domin su girbi abinda suka shuka."
"Tserewa suka yi daga wurin yayin da suka hangi jami'an tsaro na zuwa, amma da sanya hannun su aka kashe musulmai 22 tare da raunata wasu 14 kafin su bar wajen."

"Bazai yuwu ace mutun shida kacal da aka kama ne suka aikata kisan ba. Mutum shida ba zasu iya aikata haka ga mutanen da suka cika motocin bas biyar ba. Ya zama wajibi a kamo sauran."

Bamu yarda da Lalong da Akeredolu ba

MURIC ta nuna rashin yarda da maganganun gwamnan Filato, Simon Lalong da kuma na Ondo, Akeredolu.

MURIC tace:

"Sam bamu yarda da maganar gwamnan Filato, Lalong, da na Ondo Akeredolu, ba, waɗanda suka ce harin ya faru ne bisa kuskure."
"Wannan uzurin alama ce ta akwai bakin shugabanni a harin. Abun kunya ne Akeredolu ya saka kabilanci a lamarin kisan yan asalin jiharsa don kawai su musulmai ne."
"Ta ya ma wani zai ce musulmai masu ɗumbin yawa daga Ikare jihar Ondo za'a kashe su saboda kuskuren bayanai? Wannan soki burutsu ne kawai, tunani ma bazai iya ɗauka ba."
"Su wa yan ta'addan kiristoci suke da damar kashewa kuma suwa zasu kyale? Wannan irin uzurin ya fallasa rashin tunanin gwamnonin biyu. Kawai suna zubda hawayen karya ne."

Muna son IGP ya jagoranci Bincike

MURIC ta kuma nemi a baiwa Sufeto Janar na yan sandan ƙasar naan ya jagoranci bincike kan lamarin domin Gwamna Lalong ba abun yarda bane.

MURIC tace:

"Muna bukatar sanin inda aka kwana kan kisan Janar Alkali, ina waɗanda aka kama da hannu a kisan, kuma ina shari'a ta kwana? musulman Najeriya na bukatar sanin inda aka kwana."
"Komai ya fito fili daga faruwar wannan lamarin cewa matafiya musamman musulmai ba su da tsaro a hanyar Jos."
"Muna kira ga yan uwa musulmai, musamman na garin Ikare da Bauchi, inda aka yi zikirin da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu biyayya ga doka."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan mulumai a Jos yace harin shiryayye ne ga abinda aka hara.

Shugaban ya kuma umarci hukumomin tsaro da su gaggauta kamo duk wani mai hannu a kisan matafiyan, ya kuma kara da cewa baya son kurkure kan lamarin.

Buhari yace sanannen abu ne jihar Filato na ɗaya daga cikin jihohin da rikitin addini da na makiyaya da manoma ya saba faruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel