Wannan Shiryayyen Kisa Ne, Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai da Kisan Musulmai a Jos

Wannan Shiryayyen Kisa Ne, Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai da Kisan Musulmai a Jos

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da kisan matafiya musulmai a Jos
  • Buhari yace wannan shiryayyen harin kisa ne, kuma gwamnatinsa ba zata ɗau lamarin da sauki ba
  • Fadar shugaban ta nuna jin daɗinta bisa yadda manyan masu faɗa aji suke ta kokarin kwantar da tarzomar

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan matafiya ranar Asabar a jos, waɗanda suka dawo daga taron Addini.

Sannan kuma Buhari bai ji daɗin rahoton kashe akalla mutum 22 daga ciki ba tare da raunata wasu yayin da suke kan hanyar komawa gida.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar a shafin Facebook ranar Asabar.

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
Wannan Shiryayyen Kisa Ne, Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai da Kisan Musulmai a Jos Hoto: @Buharisallau
Asali: Instagram

Buhari yace sanannen abu ne jihar Filato na ɗaya daga cikin jihohin da rikitin addini da na makiyaya da manoma ya saba faruwa.

Kara karanta wannan

Abinda Shugaba Buhari Zai Fara Yi Bayan Dawowarsa Daga Landan, Femi Adesina

Amma an samu saukin lamarin biyo bayan ɗaukar matakai da kuma kokarin gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Simon Lalong.

Wannan shiryayyen abu ne

Shugaban yace bisa yadda aka shirya kai harin, ya nuna a fili cewa an tsara tare da shirya kai farmaki ga sanannen abun hari, wuri da kuma addini amma ba mamaya ba ce sam.

Wani sashin jawabin yace:

"Fadar shugaban ƙasa na mika sakon ta'aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe kuma zata cigaba da bibiyar halin da ake ciki tare da hukumomi, da suka haɗa da jami'an tsaro da na gwamnati."
"Ba zamu amince da kaiwa yan kasa irin wannan hari ba, kuma ya saɓa wa koyarwar addinan ƙasar mu baki ɗaya."

Bana son kuskure a kamo duk masu hannu, Buhari

Shugaba Buhari ya bayyana cewa yana tare da musulmai da kiristoci wajen Allah wadai da lamarin, kuma sai an hukunta duk masu hannu.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

Buhari yace:

"Bana son kuskure kan wannan harin: na yi wa yan Najeriya alƙawarin kare rayuwarsu. Na umarci hukumomin tsaro da su kamo masu hannu a wannan harin kisan gilla da aka yi wa matafiyan da basu ji ba su gani ba."

Fadar shugaban ƙasa ta yaba da kokarin gwamnan Filato, sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abukar, Sheikh Dahiru Bauchi da kuma wasu shugabannin kiristoci da na musulmai a kokarin da suke na kwantar da hankalin al'umma.

A wani labarin kuma gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, ya bayyana yadda yake shan matsin lamba daga iyalai da abokan arziki kan takarar shugaban ƙasa.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin wasu ƙungiyoyi dake neman ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023.

Muhammed, wanda ya nemi a bashi mako 3 ya yi shawara, ya sake neman a sake ba shi lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262