Da dumi-dumi: Tsohon shugaban kasa na mulkin soja IBB ya yi waje da Atiku, Tinubu daga zaben 2023
- Tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana dalilin da ya sa bai kamata 'yan Najeriya su zabi tsofaffin 'yan siyasa ba a 2023
- Babangida, wanda ake kira IBB, ya fada a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta, cewa kasar na bukatar wani matashi mai kwazo da zai karbi mulki daga hannun Buhari
- A cewarsa, Najeriya tana da albarkatu na dan adam da kasa don canza kasar ba tare da taimakon kasashen waje ba
Minna, jihar Neja - Burin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar na son zama shugaban kasa a 2023, na iya haduwa da cikas.
Gidan talabijin na Arise TV ya ruwaito cewa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bukaci 'yan Najeriya da kada su zabi duk wanda ya haura shekaru 60 a matsayin shugaban kasa a babban zabe mai zuwa.
2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari
Legit.ng ta tattaro cewa daga Atiku har Asiwaju, wanda shine tsohon gwamnan jihar Legas tsakanin 1999 zuwa 2007, za su cika shekaru 70 da doriya a shekarar 2023.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, wanda ya cika shekaru 75 a wannan shekara zai cika shekaru 77, yayin da Tinubu, wanda ya yi bikin cika shekaru 68 a hukumance a watan Maris, zai cika shekaru 70 a babban zabe mai zuwa.
IBB ya ce kada a bari wanda ya haura shekaru 60 ya zama Shugaban kasar Najeriya
Babangida, wanda ya ce kasar tana da albarkatun dan adam da na kasa, ya yi nuni ga wasu mutane kalilan da ya ce sun kai shekaru 60, suna da ikon zama shugaban kasa da kuma iya gudanar da mulkin kasar yadda ya kamata.
Da yake magana a wata hira ta musamman a gidan talabijin din a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta, IBB ya ce daya daga cikin dalilan da yasa Najeriya ta ki ci gaba da cimma burin magabatanta da suka kafa ta shine saboda ‘yan Najeriya sun yanke kauna da makomar kasarsu.
Tsohon shugaban, wanda ya zargi mutanen Najeriya da kirkira da kuma ruguza kasarsu, ya bayyana rashin shugabanci mai kyau a matsayin babban dalilin kalubalen zamantakewa da tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta.
Da yake magana game da 'yan takarar shugaban kasa na 2023, IBB ya ce sun kasance mutane 'yan shekaru 60 tare da abokan hulda a duk fadin kasar kuma wadanda ke ratsa shiyyoyin siyasa na tallata karbuwa da karfin su.
2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari
A gefe guda, 'Yan siyasar Najeriya daga yankin kudu maso gabas sun yi amanna kan cewa lokaci ya yi da za a bai wa matasa ragamar kula da shugabancin kasa.
Wadanda suka gabatar da wannan ra'ayi a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, yayin wani shiri na Jakadan Matasan Najeriya a kasashen waje (NDYA) wanda aka shirya a Abuja sun hada da Sanata Eyinnaya Abaribe, Rochas Okorocha, da Orji Kalu da sauransu.
Asali: Legit.ng