Yan bindiga sunfi IPOB da Igboho hatsari - Tsohon Sanata

Yan bindiga sunfi IPOB da Igboho hatsari - Tsohon Sanata

  • Tsohon Sanata ya bayyana yadda yan bindiga suka fi IPOB da Igboho hatsari
  • Ya fadi haka ne a wata tattaunawa da yan Jarida
  • Ya kuma yabawa gwamnatin Kaduna kan wanke Sheikh Ibrahim El Zakzaky da matarsa

Kaduna - Shehu Sani, Tsohon sanata wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisa ta takwas kuma tsohon ciyaman a Kwamitin basussuka na gida da waje ya nuna yadda yan bindiga suka fi IPOB da Igboho hatsari.

A wata tattaunawa da Jaridar The Sun tsohon sanatan ya bayyana cewa da lokacin da gwamnatin tarayya take batawa wurin yakar yan aware, shi tayi amfani da shi wurin yakar yan ta'adda toh da an samu sukuni da tsaro arewa maso gabashin kasar.

Yan bindiga sunfi IPOB da Igboho hatsari - Tsohon Sanata
Yan bindiga sunfi IPOB da Igboho hatsari - Tsohon Sanata Source: Twiiter
Asali: Twitter

Ga abinda yace game da aikin yan bindiga

"Jihar Kaduna a kewaye take da ayyukan yan bindiga, suna talauta mutanenmu wanda hakan yake tilasta musu saida gidajensu, filaye da wasu kadarori domin kawai su biya kudin fansan yanuwansu da aka sace.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari wani kauye, sun yiwa mai gari yankan rago

Sun lalata tsarin noma wanda hakan yasa manona basa iya zuwa gonakinsu.
Tsarin Ilimi duk ya lalace saboda zaluncin wadannan mutane.
Har lalacewar ta kai suna karban haraji a wasu wurare. Sun riga sun zama jiha a cikin jiha, Wannan shine abin bakin .cikin da muka tsinci kanmu a yau
Garkuwa da mutane ya zama sana'a a Arewa ta yamma a kasarnan, sun riga sun zama shugabannin kansu.
A jiharmu Kaduna, ba ranar Allah da zata fadi da bazaka a ruwaito anyi garkuwa da mutane ba.
Sai anyi garkuwar mai yawa ma kake ji ba na uku ko mutum hudu ba.idan suka sace mutum, sannan aka ki biyan kudin fansa kan lokaci sai su siyar da mutumin ga wasu masu garkuwar wanda zai kara kudin fansan da za'a biya.
Ya kamata gwamnati ta rika tattaunawa da yan bindigan nan, ta haka ne kawai zamu kawo karshen matsalar nan."

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

An Kama Wanda Ake Zargi Da Ɗaukan Nauyin Ƴan IPOB/ESN, Da Wasu Mutum 25 a Otel

A bangare guda, yan sandan jihar Imo sun ce sun kama wani mutum da aka ce ya amsa cewa yana daga cikin masu daukan nauyin ayyukan kungiyar masu son kafa Biafara wato IPOB da ESN, Daily Trust ta ruwaito.

Ana kyautata zaton Boniface Okeke ya bada gudunmawar a kalla Naira miliyan 10 ga kungiyar IPOB, a cewar mai magana da yawun yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abbatam cikin wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel