Kai tsaye ta gidan talabijin, ministan Buhari yana rokon 'yan bindiga alfarma

Kai tsaye ta gidan talabijin, ministan Buhari yana rokon 'yan bindiga alfarma

  • Chukwuemeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi, ya roki 'yan bindiga da su taimaka su daina sace dalibai
  • Ministan ya sanar da hakan ne yayin nuna jin dadinsa kan labarin sako daliban makaranta Bethel 3 da aka yi
  • Ya tabbatarwa da iyayen dalibai cewa babu shakka za a tabbatar da an ceto 'ya'yansu daga miyagun 'yan bindiga

Abuja - Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, yayi kira ga 'yan bindiga da su hakura kuma su taimaka su daina sace dalibai.

Ministan yayi wannan kiran ne yayin da ya bayyana a shirin siyasarmu a yau ta gidan talabijin na Channels.

An tambaya ministan kan tsokacin da zai iya yi kan dalibai uku na makarantar Bethel Baptist da 'yan bindigan suka sako a jihar Kaduna.

Kai tsaye ta gidan talabijin, ministan Buhari yana rokon 'yan bindiga alfarma
Kai tsaye ta gidan talabijin, ministan Buhari yana rokon 'yan bindiga alfarma. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ministan ilim ya roki 'yan bindiga Allah da Annabi

Ina farin ciki, irin wadannan labaran nake son ji a kowacce rana. Su dawo mana da yaranmu. Ina yi wa yaran farin ciki tare da iyayensu, amma ina roko kuma zan cigaba da roko.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kutsa Wurin Ibada Sun Hallaka Babban Malami Yana Tsaka da Addu'a

Na je Katsina domin in roki dakarun sojinmu dake tuka jiragen sama zuwa wuraren nan da su dage kuma suna kokarin bibiyar masu garkuwa da mutane. Amma kuma ina rokon 'yan bindigan da duk wanda suke jin maganarsa, da su taimaka su bar mana yaranmu.
A halin yanzu muna da matsaloli daban-daban, daga Kagara zuwa Jangebe, duk sun hana yara zuwa makaranta. Wannan bai dace ba. Rashin tsaro babbar matsala ce dake hana karatu.
Ina farin cikin dawowar wadannan ukun gida kuma zan yi farin ciki idan sauran suka dawo

Minista ya tabbatarwa iyaye za a ceto 'ya'yansu

Nwajiuba ya kara da tabbatarwa da iyayen dalibai cewa gwamnati za ta yi duk abinda ya dace wurin tabbatar da an sako yaransu da aka sace.

Sama da dalibai 900 a halin yanzu ke hannun 'yan bindiga bayan sun sace su daga makarantunsu.

Duk da tabbacin da gwamnatin tarayya ta cigaba da baiwa jama'a na bada kariya, miyagu sun cigaba da gallazawa jama'a.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Kaduna daga 'yan bindiga

Abinda ya hana mu ceto daliban makarantar Tegina, Gwamnatin Neja

Gwamnatin jihar Neja ta bayar da dalilan da zasu iya janyo bacin lokaci wurin ceto yaran makarantar islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina.

Yayin da sakataren jihar, Ahmed Matane, yake tattaunawa da ThisDay a ranar Litinin, ya bayyana yadda iyayen yaran suka dakatar da amfani da sojoji wurin ceto yaran.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta so amfani da sojoji wurin shiga dajin su bude wuta su ceto yaran amma iyayen yaran sun dakatar dasu saboda gudun rasa rayukan yaran garin yin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel