Da Duminsa: Benin Ta Faɗi Ranar da Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Baiwa Sunday Igboho Mafaka

Da Duminsa: Benin Ta Faɗi Ranar da Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Baiwa Sunday Igboho Mafaka

  • Lauyan shugaban yan awaren kafa kasar yarbawa Sunday Igboho, ya bayyana cewa suna tsammanin a bashi mafaka
  • Hukumomi a kasar Benin sun damke Igboho ne tare da matarsa yayin da yake kokarin tserewa Germany
  • Kasancewarsa a jamhuriyar Benin na aƙalla awanni 24 yana da damar neman a bashi mafaka a kasar

Benin Republic: Akwai alamu masu karfi cewa Benin zata bayyana sakamakon bukatar baiwa jagoran masu fafutukar kafa kasar yarbawa, Sunday Igboho mafaka a wannan makon.

Punch ta rahoto cewa lauyoyin Igboho sun dakatar da neman belinsa saboda rahoton asibiti da kuma sakamakon ba shi mafaka da suke tsammani.

Rahotanni sun bayyana cewa lauyoyin Igboho na duba hanyoyi da dama domin fitar da shi kuma ba tare da an dawo da shi Najeriya ba.

Sunday Igboho
Da Duminsa: Benin Ta Faɗi Ranar da Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Baiwa Sunday Igboho Mafaka Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An kame Sunday Igoboho da matarsa a ranar 19 ga watan Yuli a filin jirgin sama dake Kwatano yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Germany.

Wannan ya biyo bayan harin da jami'an DSS suka kai gidansa a Ibadan kuma suka bayyana nemansa ruwa a jallo, kamar yadda punch ta ruwaito.

Shin Benin zata iya baiwa Igboho mafaka?

Yayin da aka sake gurfanar da shi a gaban kotu ranar Litinin da ta gabata, an sake gabatar da sabbin tuhume-tuhume a a kansa.

Shugaban tawagar lauyoyin Igboho, Olasupo Ojo, yace har yanzun bai samu rahoto a hukumance ba.

Da aka tambayeshi ko an baiwa Igboho mafaka a Benin, yace:

"Ban sami wani labari daga gare su a hukumance ba dangane da wannan tambayar taku, amma muna tsammanin sanin sakamakon bukatar a wannan makon.

Hakazalika, Ibrahim Salami, ɗaya daga cikin lauyoyin Igboho yan asalin kasar Benin, yace idan har aka ba shi mafaka a kasar, to za'ai watsi da duk wata kara da aka shigar akan shi.

Salami ya faɗi hakane yayin da yake bayanin cewa ba'a kama Igboho yana kokarin mallakar Fasfon Benin ba kasancewarsa ba ɗan kasa ba.

Lauyan yace:

"Da ya tsero daga Najeriya ya biyo ta ɓarauniyar hanya zuwa Benin. Jami'an tsaron filin jirgi ne suka dakatar da shi kasancewar ya shiga sahun waɗanda ake nema ruwa a jallo."
"Bai karya wata dokar kasar Benin ba kuma basu kama shi da fasfon Benin ba. An kama shi ɗauke da fasfon Najeriya da kuma katin zama ɗan ƙasar Germany, saboda haka ba ya bukatar wata biza a a kan haka."
"Da muka yi nazari kan shari'ar sa, mun gano cewa gwamnatin Najeriya bata shigar da ƙarar bukatar maida shi Najeriya ba, kawai sun faɗi cewa Najeriya na neman shi ruwa a jallo bisa aikata wasu manyan laifuka."

Salami ya ƙara da cewa babu wata cikakkiyar shaida ta cewa shi mai laifi ne, kuma ya ɗauki tsawon wanni 24 a Benin saboda haka ya bukaci mafaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel