'Yan Sanda Sun Sheke Fitaccen mai Satar Jama'a da ya Saci Mahaifinsa ya Karba N4m na Fansa

'Yan Sanda Sun Sheke Fitaccen mai Satar Jama'a da ya Saci Mahaifinsa ya Karba N4m na Fansa

  • Jami'an tsaro a Kogi sun sheke hatsabibin mai garkuwa da mutane a Kogi da ya dade yana addabar yankin
  • An gano cewa fitaccen mai garkuwa da mutanen ya taba sace mahaifinsa kuma ya karba miliyan hudu kudin fansa
  • Tawagar hadin guiwa ta jami'an tsaron har ila yau sun cafke wani Kizito wanda ya addabi jihar Kogi da Benue

Olamaboro, Kogi - Jami'an tsaro dake karamar hukumar Olamaboro ta jihar Kogi a ranar Asabar sun sheke wani gagararren mai garkuwa da mutane bayan musayar ruwan wuta da suka yi.

An gano cewa hatsabibin ya taba sace mahaifinsa kuma sai da ya karba kudi har naira miliyan hudu na fansa kafin ya sako shi, prnigeria ta ruwaito.

An san mamacin da hannu a cikin garkuwa da mutane tare da fashi da makami kuma jami'an tsaro sun dade suna nemansa amma sai a wannan lokacin ne dubunsa ta cika.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama

KU KARANTA: An gano makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara

'Yan Sanda Sun Sheke Fitaccen mai Satar Jama'a da ya Saci Mahaifinsa ya Karba N4m na Fansa
'Yan Sanda Sun Sheke Fitaccen mai Satar Jama'a da ya Saci Mahaifinsa ya Karba N4m na Fansa. Hoto daga Vanguardngrnews.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Rick Ross: Mawakin gambara da ya mallaki motoci 100 na alfarma, bashi da lasisin tuki

Tawagar hadin guiwa ta jami'an tsaro ta cafke Kizito

Hakazalika, an gano cewa wata tawagar hadin guiwa ta jami'an tsaro da suka samu shugabancin shugaban karamar hukumar Olamaboro, Honarabul Adejohh Friday Nicodemus sun damke wani mai suna Kizito Ocheme wanda ya shahara a satar jama'a.

Kamar yadda prnigeria ta wallafa, dan ta'addan ya saba sata da addabar jama'a a tsakanin kananan hukumomin Olamaboro da Otukpa ta jihar Benue amma sai aka kama shi yayin da yake kokarin tserewa.

Mene ne babban burin Yahaya Bello?

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa Gwamna Yahaya Bello da dukkan shugabannin gwamnatin jihar Kogi sun tabbatar da cewa zasu baiwa rayuka da kadarori kariya kuma miyagu ba zasu taba samun wurin zama a Kogi ba.

Kara karanta wannan

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

Ya kara da cewa, daga cikin umarnin Gwamna Bello shine jama'a sun cacanci zaman lafiya, gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai burin gwamnan na samar da zaman lafiya ya tabbata.

'Yan bindiga sun kai farmaki babban asibiti a Zamfara

Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kutsa babban asibiti gwamnati dake Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Juma'a.

Daily Trust ta tattaro cewa miyagun sun yi awon gaba da wata ma'aikaciyar jinya da kuma wata mai jinyar mara lafiya.

Mazauna yankin sun sanar da cewa bayan 'yan bindigan sun shiga asibitin, 'yan bindigan sun fara neman likita ko ma'aikatan jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel