Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama

  • Wasu mutane ɗauke da makamai da ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe mutum 4 a wasu kauyukan Filato
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun farmaki kauyukan dake karamar hukumar Bassa yayin da mutane ke bacci
  • A halin yanzun an tura jami'an tsaro da dama yankin domin dawo da zaman lafiya da kuma bincike

Jos, Plateau:- Wasu yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kai hari wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Bassa, jihar Filato, kamar yadda punch ta ruwaito.

Yayin harin yan bindigan sun hallaka mutum huɗu tare da ƙona gidajen mutane da dama, kamar yadda this day ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa harin, wanda ya bar mutane da dama cikin raunuka, ya faru ne lokacin mutane na bacci ranar Asabar da daddare.

Yan bindiga sun kai hari kauyukan Filato
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Plateau, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wace irin ɓarna maharan suka yi?

Shugaban ƙungiyar cigaban Irigwe, Ezekiel Bini, shine ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Lahadi a Jos.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tawagar Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu Yayin Sace Mace Mai Juna Biyu a Sokoto

Mr. Bini yace:

"Fulani makiyaya sun sake kaiwa mutanen mu hari a daren da ya gabata, amma wannan harin abin damuwa ne matuka."
"Sun ƙona gidaje da dama a ƙauyen Zamuna da kuma gidajen dake kusa da Jebbu Miango. Sun lalata mana gonakin mu ta hanyar sassare shukoki sannan suka cinnawa gidaje wuta."
"Zuwa yanzun an tabbatar da mutuwar mutum huɗu yayin da wasu da dama suka ji raunuka."

Legit.ng hausa ta gano cewa an jibge jami'an tsaro a yankin da lamarin ya faru domin ɗaukar matakin da ya dace.

ISWAP sun mamayi sojoji sun buɗe musu wuta

A wani rahoton na daban kuma Yan Ta'addan ISWAP Sun Mamayi Sojoji Sun Bude Musu Wuta a Borno

Gwamman yan ta'addan ISWAP sun yi wa jerin gwanon sojoji kwantan bauna suka bude musu wuta a hanyar Gubio/Damasak ranar Asabar.

Jami'an sojojin sun faɗa tarkon yan ta'addan ne yayin da suke kan hanyar zuwa Gobio domin ɗakko mambobin APC zuwa taronsu dake gudana a Damasak.

Kara karanta wannan

Jihar Neja: An tsare daliban Tegina da aka sace a sansanoni 25

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262