Saura awanni 48 ayi zabe, an taso Mai Mala Buni da 'yan kwamitinsa su ajiye shugabancin APC

Saura awanni 48 ayi zabe, an taso Mai Mala Buni da 'yan kwamitinsa su ajiye shugabancin APC

  • Akwai yiwuwar a sauke kwamitin Gwamna Mai Mala Buni a jam’iyyar APC
  • A doka bai halatta wani mai rike da mukamin Gwamnati ya rike jam’yya ba
  • Hukuncin kotun koli kan zaben Ondo ya nuna CECPC ba ta da gindin zama

Abuja - Hukuncin da Alkalan kotun koli suka bada a game da shari’ar zaben gwamnan jihar Ondo, ya dawo da duk wasu shiri na jam’iyyar APC baya.

Jaridar Daily Trust ta ce hukuncin da aka zartar a ranar Laraban, ya jawo wasu sun fara kiran a ruguza kwamitin rikon kwarya na APC mai mulki.

Hukuncin Alkalan kotun koli

Shari’ar zaben gwamnan na jihar Ondo ya raba kan Alkalan kotun koli, inda Alkalai uku suka ba Eyitayo Jedege gaskiya, hudu suka tabbatar da nasarar APC.

Alkali Mary Odili ta zartar da cewa nada Mai Mala Buni a matsayin shugaban jam’iyyar APC ya saba wa sashe na 183 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999.

Kara karanta wannan

Bayan APC ta sha da kyar a kotu a zaben Gwamna, Minista ya ce za a iya rasa zaben 2023

Hadiman Buhari sun huro wa CECPC wuta

A ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, 2021, mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu ya nuna goyon bayan ruguza CECPC.

Haka zalika Sanata Ita Enang, wanda shi ne ke ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkokin Neja-Delta ya na goyon bayan wannan matsaya.

Shugabannin APC
Mai Mala Buni da Buhari Hoto: gazettengr.com
Asali: Twitter

Ita Enang da Babafemi Ojudu sun yi magana da Daily Trust, suka ce hukuncin kotu ya ruguza duk wani halacci na kafa kwamitin rikon kwarya a jam’iyyar APC.

Hadimin shugaban kasar suka ce Gwamna Mai Mala Buni da kwamitinsa ba su da hurumin da za su dauki wani mataki a madadin jam’iyyar APC mai mulki.

Masu ba shugaban Najeriyar shawara suka ce hukuncin kotun ya zo da wuri, ba don haka ba da za a iya rusa shirin jam’iyyar a lokacin da ake shirin zaben 2023.

Ra’ayin Festus Keyamo SAN

Kara karanta wannan

Wani sabon yamutsi ya na jiran Shugabannin APC a kan yadda za ayi rabon kujeru na kasa

Da jin wannan hukunci, Festus Keyamo ya shaida wa APC cewa saura kiris ‘dan takarar PDP a zaben Ondo, Eyitayo Jegede ya yi masu illa a kotun koli.

Keyamo ya na ganin nan gaba ba dole ba ne jam’iyyar APC ta taki sa’ar da ta samu yanzu. Idan aka samu bacin rana, APC za ta iya samun kanta a matsala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel