2023: Shugabannin APC na so Gwamna Lalong ya gaji Shugaba Buhari

2023: Shugabannin APC na so Gwamna Lalong ya gaji Shugaba Buhari

  • Wasu shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Filato suna kokarin ganin gwamnan jihar, Simon Lalong ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023
  • An tattaro cewa shugabannin sun gudanar da wani taro kan haka a garin Jos, inda tuni suka fara masa kamfen
  • A cewarsu Lalong ya cancanci hawa wannan kujera domin kawo ci gaba da hada kan kasa

Jos, jihar Filato- Wani rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa wasu shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Filato sun fara kulla-kulla don ganin gwamnan jihar, Simon Lalong ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Jiga-jigan jam’iyyar sun hadu jiya Talata, 27 ga watan Yuli, a Jos, babban birnin jihar, inda suka yanke shawarar marawa gwamnan baya kuma suka fara masa kamfen.

2023: Shugabannin APC na so Gwamna Lalong ya gaji Shugaba Buhari
Wasu shugabannin APC suna son Gwamna Lalong ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jagoran tawagar, Alhaji Saleh Zazzaga, wanda ya yi magana a wurin taron ya ce Lalong ya cancanci tsayawa takara, lashe zaben da kuma samar da kyakkyawan shugabanci ga ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna

Ya bayyana yadda ya gwamnan ya “dinke bambancin kabilanci da addini” a tsakanin kungiyoyi daban-daban masu akida mabanbanta a jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce:

“Saboda kyakkyawan shugabanci na Lalong, ya sa aka nada shi Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, wanda a kansa ya kasance mai gina gadar zaman lafiya, fahimta da ci gaban yankin arewa da kasa baki daya.
"Bugu da ƙari, duk da mawuyacin halin da tattalin arziki ƙasar ke ciki da raguwar kuɗaɗen shiga a jihar, Lalong ya ci gaba da biyan albashin da ba a taɓa gani ba, yayin da sauran gwamnonin jihohi ba sa iya yin hakan."

2023: Ku Tashi Ku 'Ƙwace' Mulki Daga Hannun Dattijai, Gwamna Ya Zaburar Da Matasan Nigeria

A gefe guda, Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi ya ce matasan Nigeria ba su nuna wa dattijai cewa 'lallai da gaske suke son karɓe shugabancin kasa ba', rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo

Bello, wanda tuni ya bayyana niyyarsa na yin takarar shugabancin kasa, a ranar Talata ya yi kira ga matasa su yi aiki don ganin sun 'ƙarbe' mulki daga hannun dattawa gabanin zaben 2023.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a Ijebu-Ode, jihar Ogun, a wurin wani taro da aka yi wa laƙabin: 'Matasa ke da iko a hannun su'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng