Yadda 'yan sanda suka cafke wani da ake zargin yana karbar kudin fansa ta asusun banki
- Rundunar 'yan sanda sun cafke wani mutum da ake zargin ya karbi kudin fansa ta asusun banki
- Rahoto ya bayyana yadda aka yi dambarwa a ofisihin 'yan sanda don kokarin warware zaren
- Lamari ya ki warwaruwa, an tura gaba domin tantace abin da ya kamata a yi don samun mafita
Rundunar ‘yan sanda a Suleja, Jihar Neja, ta cafke daya daga cikin wadanda ake zargin mai satar mutane ne da ke karbar kudin fansa ta banki a Babban Birnin Tarayya (FCT).
Wannan kenan kamar yadda mai asusun bankin da mai garkuwa da mutanen ya yi amfani da shi, Babawi Abba, ya dauki lauya don ya kare kansa domin ya tabbatar da cewa ba shi da laifi a cikin lamarin.
Daily Trust ta ruwaito cewa mijin daya daga cikin wadanda aka sace, Saheed Adewuyi cewa, ya biya N500,000 a cikin wani asusun bankin Access mai lamba 1403762272 da suna Badawi Abba Enterprise.
Rahoton ya ce ba a kama mai asusun ba, kuma ba a daura masa ankwa ba.
A halin yanzu, rundunar 'yan sanda ta gayyaci Mista Adewuyi don yin bayani a kan lamarin.
Bayan haka Kwamandan yankin ya umarci Insp. Idris, dangin wanda ake zargi da satar da kuma lauya don sasanta lamarin da Adewuyi, amma shi (Adewuyi) ya ce ba batunsa ba ne kuma saboda haka, babu abin da za a sasanta.
Bangarorin, ciki har da ‘yan sanda, sun ci gaba da rarrashin Adewuyi don ba da damar batun ya mutu, suna bayyana cewa wanda ake zargin ba mai laifi bane.
A nasa bangaren, Adewuyi ya roki 'yan sanda su sa wanda ake zargin ya gabatar da wasu wadanda ake zargi da ya ba su kudi bayan ya cire su.
Shima da yake magana, Abba, mai asusun, ya bayyana cewa bai san komai game da lamarin ba har sai da bankinsa, Access ya tuntube shi don sanar dashi abin da ke faruwa, inda ya kara da cewa nan take ya tuntubi lauyansa don taimaka masa da mafita.
Ya ce zai iya tuna cewa a watan Yuni, da gaske ya bayar da bayanansa na banki ga wani da ke gudanar da kasuwancin hada-hadar kudi ta POS kusa da shagonsa a mashahurin kasuwar Ibrahim Badamosi Babangida, Suleja, Jihar Neja.
Wani jami’in ‘yan sanda, a lokacin da yake zantawa da wakilin Daily Trust bisa sharadin kada a bayyana sunansa, ya ce 'yan sanda a baya sun gano batutuwan satar mutane da yawa amma wasu manyan ’yan siyasa a kasar sun rufe ta.
Jami'in 'yan sanda masu bincike (IPO) na karar, Insp. Idris ya fadi cewa za a mika karar zuwa sashen yaki da satar mutane a Minna, babban birnin jihar Neja.
Bayan hallaka DPO, 'Yan sanda sun sake cafke wani bokan kungiyar ta'addanci ta IPOB
Tawagar wasu 'yan sanda na rundunar 'yan sanda ta jihar Imo ta cafke bokan da ke shirya layu ga mambobin kungiyar IPOB da ESN a cikin Jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.
Wanda ake zargin, Benneth Okoli, mai shekaru 49, an kama shi ne a hubbarensa da ke Akuma a karamar hukumar Oru ta Gabas ta Jihar ta Imo.
A yau Alhamis 29 ga watan Yuli ne aka gurfanar da wanda ake zargin a hedikwatar rundunar 'yan sanda da ke Owerri bayan gudanar da binciken kwakwaf da tattara bayanan sirri na cewa yana shirya layu ga 'yan bindiga a hubbarensa, in ji kwamishinan 'yan sandan jihar.
Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru
A wani labarin, Majalisar Dattijan Najeriya ta ce Ma'aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da butumbutumi da basirar na'ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar, sashen Hausa na BBC ya ruwaito.
Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar.
Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020.
Asali: Legit.ng