Da duminsa: CBN ta haramta sayar da Dala ga yan kasuwan canji daga yanzu

Da duminsa: CBN ta haramta sayar da Dala ga yan kasuwan canji daga yanzu

  • CBN ta gudanar da taronta na MPC kamar yadda ta saba lokaci bayan lokaci
  • A wannan karo, CBN ta yi babban sanarwa kan Dalar Amurka
  • Babban bankin ya ce za a daina rijistan sabbin yan kasuwar canji

Babbar bankin Najeriya CBN ya haramta sayar da Dalar Amurka ga yan kasuwan canji (BDC).

Gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ne ya sanar da hakan a jawabin da ya yiwa manema labarai bayan zaman kwamitin kudi MPC na bankin, rahoton DailyTrust.

Ya ce N5. 7 billion da ake baiwa yan kasuwar canji ba zai yiwu a iya cigaba ba saboda kimanin yan kasuwan canji 5500 ake baiwa $110million kowani mako.

Ya kara da cewa CBN za a daina rijistan sabbin yan kasuwar canji.

Daga yanzu, bankuna za'a koma saye da sayar da dala kuma bankunan zasu samar da ofis na musamman don haka.

Da duminsa: CBN ta haramta sayar da Dala ga yan kasuwan canji daga yanzu
Da duminsa: CBN ta haramta sayar da Dala ga yan kasuwan canji daga yanzu
Asali: Original

Legit ta zanta da wani ma'aikacin wani babban banki a Najeriya, Mr Yusuf Abdullateef, wanda ya bayyana ra'ayinsa kan wannan sabon sanarwa na bankin CBN.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 Da Ta Yi Wu Baka Sani Ba Game Da DCP Abba Kyari

A cewarsa, wannan mataki ne da ya dace illa akwai wasu kalubale da hasashen matsaloli dake tattare da hakan.

Yace:
"Ni a ra'ayin abune mai kyau a mayar farashin sayar da Dala guda daya kacal sabanin yadda abin yake inda banki ya banbanta da na kasuwar fagge, amma shin CBN zai samar da isasshen Dala ga bankuna don sayarwa mutane?."
"Yan kasuwan canji ne yanzu fa ke sayarwa mutane Dala saboda CBN ta hana sayarwa daidaikun mutane Dalar Amurka na tsawon lokaci yanzu, illa manyan kamfanoni masu bukatar shigo da kaya, sai kuma masu son biyan kudin makarantar yaransu dake kasashen waje."
"Matsalar dai yanzu shine farashin canjin Naira zuwa Dala zai tashi na dan lokaci a kasuwar bayan fagge."

Asali: Legit.ng

Online view pixel