Abubuwa 10 Da Ta Yi Wu Baka Sani Ba Game Da DCP Abba Kyari

Abubuwa 10 Da Ta Yi Wu Baka Sani Ba Game Da DCP Abba Kyari

Mataimakin kwamishinan yan sanda Abba Kyari a ranar Alhamis ya musanta cewa ya taba neman cin hanci ko karbar cin hanci daga fitaccen dan damfarar intanet Ramon Olowunwa Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi, daga cikin $1.1m na zamba.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kyari ya ce wadanda ke murna game da zargin da ake masa za su gamu da bacin rai don bai aikata wani laifi ba.

A cewarsa Hushpuppi ya taba ganin wasu kaftani da ya saka a hotunansa a dandalin sada zumunta ya tambaye shi wanda ya dinka masa ya kuma hada shi da tailan.

Abubuwa 10 Da Ta Yi Wu Baka Sani Ba Game Da DCP Abba Kyari
Abubuwa 10 Da Ta Yi Wu Baka Sani Ba Game Da DCP Abba Kyari. Hoto: Abba Kyari
Asali: UGC

Bayan an kammala dinkin an kai kayan ofishinsa da ke Abuja inda Hushpuppi ta tura aka karbar masa sannan ya kuma biya telan N300,000 kudinsa ta asusun ajiyar tailan.

Ga wasu muhimman abubuwa 10 da ta yi wu ba ku sani ba game da Abba Kyari kamar yadda The Nation ta tattaro:

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka cafke wani da ake zargin yana karbar kudin fansa ta asusun banki

  1. An haifi Kyari a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 1975.
  2. Mataimakin kwamishinan yan sanda ne kuma mamba na tawagar Sufeta Janar na Yan sandan, Nigeria, IGP-IRT, a hedkwatar yan sandan Nigeria da ke Abuja.
  3. DCP Kyari mamba ne na kungiyar shugabannin yan sanda na kasa da kasa (IACP)
  4. Kafin nadinsa a tawagar IGP-IRT, ya yi aiki a rundunar yan sanda ta jihar Legas mai kula da tawaga ta musamman masu yaki da yan fashi (SARS).
  5. Kyari ya yi fice ne bayan ya yi nasarar kama fitaccen mai garkuwa da mutane Evans da Wadume da wasu saura.
  6. Abba ya shiga makarantar horas da yan sanda da ke Wudil, Kano, a shekarar 2000.
  7. Ya kammala makarantar a matsayin mataimakin sufritandan yan sanda, ASP, aka kuma tura shi jihar Adamawa inda ya yi aiki na shekara daya a ofishin yan sanda na Song.
  8. Daga bisani an tura shi jihar Adamawa a matsayin DCO a Numan kuma ya yi aiki a matsayin kwamandan tawaga ta 14 PMF a Yola.
  9. Ya koma rundunar yan sandan Legas a matsayin 2 IC sannan daga bisani ya zama shugaban tawagar ta musamman na (SARS).
  10. Yana da aure kuma Allah ya albarkace shi da yara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Amurka Ta Bada Umurnin a Kamo Mata DCP Abba Kyari

Kotun Amurka Ta Bada Umurnin a Kamo Mata DCP Abba Kyari

A wani rahoton mun kawo muku cewa wata kotu da ke Amurka ta bada umurnin a kamo mataimakin kwamishinan yan sanda a Nigeria, DCP Abba Kyari, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewar takardan kotun da Peoples Gazette ta gani, Otis Wright na kotun Amurka na jihar California ta umurci Hukumar Bincike na FBI ta kamo Kyari ta kawo shi Amurka don ya amsa tambayoyi kan rawar da ya taka game da laifin da Ramon Abbbas (Hushpuppi) da abokansa suka yi.

The Punch ta ruwaito cewa Hushpuppi ya ce ya yi amfani da Kyari wurin kama da daure abokin laifinsa, Chibuzor Vincent, bayan Vincent ya yi barazanar fallasa zamba da suka yi wa wani dan kasuwan Qatari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel