Masoya Atiku a jihar Kano sun fara rabawa Kanawa burodi da sunan kamfe

Masoya Atiku a jihar Kano sun fara rabawa Kanawa burodi da sunan kamfe

  • Wasu masoya Atiku a jihar Kano sun fara rarraba burodi mai suna 'Atiku Kawai' da sunan kamfen
  • 'Yan Najeriya ba suyi shuru game da wannan ba, tuni suka fara tofa albarkacin bakinsu kan lamarin
  • Ana sa ran Atiku Abubakar zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023, duk da cewa ana kan dambarwar cancantarsa

Masoya ga tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, sun fara rarraba burodi, wanda ake wa lakabi da ‘Atiku Kawai’ ga mazauna Jihar Kano.

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da ake ikirarin cewa Atiku na neman tsayawa takarar shugaban kasa gabanin zaben 2023, duk da cewa bai fito fili ya tabbatar da hakan ba, SaharaReporters ta ruwaito.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya fara neman mukamin mafi girma tun shekarar 1993.

Masoya Atiku a jihar Kano sun soma rabawa 'yan jihar burodi da sunan kamfe
Burudi mai suna Atiku Kawai | Hoto: Atiku Kawai Media Group
Asali: Facebook

Ya kasance dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa ta PDP a shekarar 2019, inda ya sha ya kaye a hannun shugaban kasa mai ci manjo janar Muhammadu Buhari (Mai ritaya).

Kara karanta wannan

2023: Shugabannin APC na so Gwamna Lalong ya gaji Shugaba Buhari

Atiku ya kalubalanci nasarar da Buhari ya yi bayan zaben na shekarar 2019, a kotu amma Kotun Koli ta yi watsi da karar.

Jama'a sun tofa albarkacin bakinsu da ganin yadda ake rarraba burodin mai suna ‘Atiku Kawai’.

Ojo Oluwaseyi ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

“Burodin talauci! Ya kamata 'yan Najeriya su zama masu wayewa a yanzu. Gwamnati mai ci yanzu ta koya mana darasi mai mahimmanci kuma idan bamu koya ba yanzu ba zamu taba koyo ba."

Cisco Ekeocha ya rubuta cewa:

"Lokacin da yunwa ta yi yawa a cikin kasa, suna so su yi amfani da burodi wajen ba mayunwata cin hanci."

Abodurin Deborah ta ce:

"Kamar burodi muka zo nema a rayuwa... Shior."

2023: Gwamnatin Adamawa Ta Bada Shaida a Kan Zaman Atiku Ɗan Nigeria Ko Akasin Haka

A bangare guda da ake rikici kan takarar ta Atiku a 2023, dukkan alamu na nuna ana daf da kawo karshen dambarwar da ake yi game da cancantar Atiku Abubakar na fitowa takarar shugaban kasa a babban zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnatin Adamawa Ta Bada Shaida a Kan Zaman Atiku Ɗan Nigeria Ko Akasin Haka

The News ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Adamawa, a ranar 27 ga watan Yuli, ta shaidawa kotun tarayya da ke Abuja cewa Atiku Abubakar ya cancanta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa.

Legit.ng ta tattaro cewa attoni janar na jihar Adamawa, Afraimu Jingi, yayin gabatarwa kotu hujojinsa ya shaidawa Mai Shari'a Inyang Ekwo cewa yana son a gwamutsa shari'ar da wata kungiya ta shigar kan Atiku da wasu mutum uku.

Sanata Al-Makura ya karya jita-jitan cewa EFCC ta kame shi da matarsa, ya yi bayani

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura ya karyata jita-jitan dake yawo cewa, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi ram dashi tare da matarsa.

A jiya ne 28 ga watan Yuli jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, jami'an hukumar EFCC sun kame sanatan hakazalika sun hada da matarsa sun tafi dasu bisa zargin cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sunday Igboho ya isa kotu a Kwatano don sanin makomarsa

Amma a cewar Al-Makura, hukumar ta gayyace shi ne kan wasu korafe-korafe da ake akansa, inda ya yi tattaki yaje ofishin hukumar ya gana da shugabanta da wasu jami'anta cikin kankanin lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel