Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna

Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna

  • Miyagun 'yan bindiga sun sheke Alamkah Dominic Usman, dan takarar shugabancin karamar hukuma na APC a Kachia
  • Dominic yana kan hanyarsa ta zuwa jihar Binuwai ganin iyalinsa yayin da miyagun suka tare shi tare da sheke shi
  • Shine dan takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaben kananan hukumomi da za a yi ranar 14 ga watan Augusta

Kachia, Kaduna - Dan takarar jam'iyyar All Progressive Chairmanship Congress (APC) na karamar hukumar Kachia na jihar Kaduna, Alamkah Dominic Usman wanda aka fi sani Cashman ya sheka lahira bayan wasu miyagun 'yan bindiga sun harbe shi a jihar Benue.

A yayin zantawa da Daily Trust, shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Kachia, Alhaji Ahmed Tijjani Sulaiman, ya ce an harbe Usman a wani wuri a jihar Benue.

KU KARANTA: Tsohon kwamishina ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan daba suka kai masa farmaki

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu

Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna
Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Miyagu sun bi shahararren manomi har gonarsa sun sheke shi a Taraba

Usman yayi tafiya zuwa Binuwai, sai labarin mutuwarsa aka ji

Alhaji Sulaiman ya ce, Usman amintaccen dan jam'iyya ne kuma ya hadu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Binuwai inda iyalinsa ke zama, bai san cewa yana dab da amsa kiran ubangijinsa.

"Ba mu ji daga wurinsa ba tun bayan da ya bar Kachia daga jihar Binuwai a ranar Alhamis, sai kwatsam muka ji labarin cewa an kashe shi."

Har zuwa mutuwarsa, shine dan takarar shugabancin karamar hukuma a Kachia dake jihar Kaduna. Ana shirin za a yi zaben a ranar Asabar, 14 ga watan Augustan 2021.

Za a birne dan siyasan a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, Daily Trust ta wallafa.

EFCC ta daskarar da asusun bankin 'yar majalisa

Daga cikin binciken siyan motocin da majalisar jihar Oyo tayi, hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta daskarar da asusun bankin daraktan kudi da asusu na majalisar jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe na makokin manjon soja, matarsa da diyarsa da hatsari ya kashe

Tribune Online ta ruwaito cewa EFCC ta daskarar da asusun bankin daraktan kudi ta majalisar wacce ta ki amsa gayyatar da hukumar tayi mata.

Daraktan tana daya daga cikin jami'an majalisar da ake tuhuma bayan an mika wani korafi na cewa kakakin majalisar ya hada kai da wasu jami'an gwamnati wurin samar da tsoffin motoci a matsayin sabbi ga 'yan majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel