Matawalle ya bayyana abinda ke assasa ta'addanci a Zamfara

Matawalle ya bayyana abinda ke assasa ta'addanci a Zamfara

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya alakanta ta'addanci da rikcin makiyaya da manoma
  • Kamar yadda gwamnan ya bayyana a garin Kaduna, yace kashe shugabannin Fulani yana asassa ta'addanci
  • Gwamna Matawalle ya alakanta rashin sasancin da wasu gwamnonin arewa maso yamma da dalilin hauhawar ta'addanci

Kaduna - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya alakanta cigaban miyagun lamurran 'yan bindiga da kuma garkuwa da mutane da ake yi a jihar da rikicin makiyaya da manoma na baya.

Matawalle ya kara da cewa rashin shiga sasancin wasu jihohin arewa maso yamma da 'yan bindiga yana daga cikin dalilan dake cigaba da assasa rikici, Channels TV ta ruwaito.

KU KARANTA: Da duminsa: An sheke DPO yayin da tsagerun IPOB suka kai farmaki Imo

Matawalle ya bayyana abinda ke assasa ta'addanci a Zamfara
Matawalle ya bayyana abinda ke assasa ta'addanci a Zamfara. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Tsohon kwamishina ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan daba suka kai masa farmaki

Kashe fitattun shugabannin 'yan bindiga na assasa ta'addanci

Kara karanta wannan

Masu Fada Aji Na Arewa Ke da Alhakin Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Matawalle Ya Fallasa

Har ila yau, gwamnan wanda yace kashe fitattun shugabannin Fulani na Dansadau suna daga cikin abubuwan dake kara rura wutar ta'addanci a jihar.

Ya kara da cewa mabiyan shugabannin Fulanin Zamfara, Kebbi da Sokoto ne suka fusata kuma suke kai farmaki kan wadanda suke zargin sun kashe shugabannninsu.

Hakan yace yake zama silar hargitsin yankunan Fulani da na Hausawa inda kowacce kungiya ke kaiwa 'yar uwarta farmaki tare da kashe-kashe.

Rikicin makiyaya da manoma ya dade yana barna

A yayin magana ta bakin zababben kwamishinansa, Ibrahim Dosara yayin taron hukumomin tsaro a jihar Kaduna, Gwamna Matawalle ya ce rikicin makiyaya da manoma ya dade kuma hakan yana nakasa masarautun gargagajiya.

A cewarsa, gazawar gwamnati na shawo kan matsalar yasa wasu daga cikin miyagun suka dauka doka a hannunsu, lamarin da yasa ta'addanci yayi kamari a Zamfara.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, sauran abubuwan da suke bada gudumawa wurin karuwar rashin tsaro ta bakin kwamishinansa, sun hada da shigowa da makamai yankin arewa maso yamma ta iyakokin kasar nan.

Kara karanta wannan

Ku tsamo dukkan miyagun dake cikinku, Sarkin Muri ga shugabanni Fulani

Miyagun sun bi fitaccen manomi sun sheke a gona

Wani shahararren manomi mai suna Saminu Barjanga dake kauyen Barjanga a karamar hukumar Gasssol dake jihar Taraba ya halaka bayan wasu sun je har gonarsa sun kashe shi.

Lamarin ya kara bada tsoro tare da firgita manoman dake yankin. Daily Trust ta tattaro yadda manomin kuma fitaccen dan kasuwan ya mallaki shaguna a wurare daban-daban dake MutumBiyu, babban birnin Gassol.

A shekarar da ta gabata ne aka sace Barjanga a wannan gonar kuma an gano cewa sai da ya biya naira miliyan bakwai kafin a sake shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel