El-Rufai ya sanar da abinda suke yi da gwamnatin Nasarawa wurin ceto basaraken jiharsa

El-Rufai ya sanar da abinda suke yi da gwamnatin Nasarawa wurin ceto basaraken jiharsa

  • Gwamnatin jihar Kaduna tace tana kokari da hadin guiwar takwararta ta Nasarawa wurin ceton basarake da aka sace
  • An sace Sarkin Jaba, Gyet Muade a ranar Litinin yayin da yake gonarsa dake da iyaka da jihar Nasarawa a Jaba
  • Wakilin yankin, Sanata Zico Azeez, ya ce sace basaraken mai daraja ta daya ya bar babban gibi a masarautar

Jaba, Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna tace tana aiki tare da gwamnatin jihar Nasarawa da kuma jami'an tsaro daga jihohin biyu wurin ceto sarkin Jaba, Gyet Muade wanda miyagun 'yan bindiga suka sace a ranar Litinin, Channels TV ta wallafa.

Miyagun 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace basaraken mai shekaru tamanin da uku a duniya yayin da yake gonarsa dake yankin Gitata na jihar Nasarawa wanda ke da iyaka da Jaba a jihar Kaduna.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

Kara karanta wannan

Matar tsohon minista ta kwanta dama tana da shekaru 91 a duniya

El-Rufai ya sanar da abinda suke yi da gwamnatin Nasarawa wurin ceto basaraken jiharsa
El-Rufai ya sanar da abinda suke yi da gwamnatin Nasarawa wurin ceto basaraken jiharsa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: An sheke DPO yayin da tsagerun IPOB suka kai farmaki Imo

Gwamnatin Kaduna ta tura wakili masarautar Jaba

Kamar yadda ChannelsTV ta ruwaito, a yayin jawabi ga wasu jami'an gwamnati da hukumomin tsaro a fadarsa dake masarautar Jaba, Gwamna El-Rufai ya samu wakilcin kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan.

Ya tabbatarwa da jama'ar masarautar cewa gwamnatocin jihohin biyu zasu yi duk abinda ya dace wurin ganin an ceto sarkin da gaggawa ballantana a wannan lokacin da yake da shekaru masu yawa da kuma rashin lafiya.

A bangarensa, shugaban yankin kuma tsohon sanata, Zico Azeez, ya yi kira ga gwamnati da jami'an tsaro da su tsananta kokari wurin tabbatar da ceto basaraken wanda satarsa ta bar babban gibi a masarautar da dukkan karamar hukumar Jaba ta jihar Kaduna.

Tsohon kwamishina ya tsallake rijiya da baya

Legit.ng ta ruwaito muku yadda 'yan daba da ake zargin magoya bayan kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Oabasa sun kaiwa tsohon kwamishinan sufuri na jihar, Kayode Opeifa farmaki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Sake Sace Wani Basarake a Jihar Kaduna

SaharaReporters ta tattaro cewa an kaiwa Opeifa farmaki a gidansa dake titin Oyewole dake tashar motan Mulero, Agege, a ranar Lahadi.

Wata majiya wacce ta ga lokacin da aka kai farmakin, ta ce 'yan daban sun je kalubalantar kwamishinan kan zarginsa da ake yi da kaka gida ga masu zabe a gunduma ta D, karamar hukumar hukumar Agege.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng