Rikicin cikin gidan ya cabe, bangaren Lai Mohammed sun sa sharadin barin APC
- Bangaren Bashir Omolaja Bolarinwa sun fara maganar ficewa daga APC a Kwara
- ‘Yan tawaren na APC suna tare da Ministan labarai, Lai Mohammed a jihar Kwara
- Ba a jitu wa tsakanin mutanen gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da na Minista
Rikicin cikin gidan da ya ratsa jam’iyyar APC ya dauki wani salo, inda wasu bangaren su ke barazanar sauya-sheka, su fice daga jam’iyyar mai mulki.
‘Yan tawaren da suke tare da Ministan harkokin yada labarai da al’adu na kasa, Alhaji Lai Mohammed sun ce za su bar jam’iyya idan ba ayi sulhu ba.
Daily Trust ta rahoto bangaren Ministan suna cewa muddin uwar jam’iyya ba ta dauki matakin dinke barakarsu da AbdulRahman AbdulRazaq, za su yi waje.
Bashir Omolaja Bolarinwa ya ja-kunnen shugaban jam'iyyar APC
Shugaban ‘yan tawaren, Bashir Omolaja Bolarinwa, ya ce ka da a ga laifin kowa idan aka fice daga APC, sai shugaban rikon kwarya na kasa, Mai Mala Buni.
Bashir Bolarinwa ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi magana da ‘yan jarida a wajen wani bikin barka da sallah da ‘yan jam’iyyar suka shirya a Ilorin.
“Uwar jam’iyya ta na wasa da jihar Kwara. Mun fada masu gaskiyar halin da ake ciki, kuma da alama, ba su damu su shawo kan koke-koken da mafi yawan ‘yan jam’iyya suke yi ba, saboda kawai su nuna goyon bayansu ga abokinsu.”
“Ina so tarihi ya ajiye cewa idan aka yi ta dandazo ana barin APC a Kwara, ka da a ga laifin kowa sai Mai Mala Buni da mutanensa.”
Alhaji Bashir Bolarinwa yake cewa da guminsu aka kafa APC a jihar Kwara, amma an yi watsi da su.
Jam'iyyar APC za ta iya rasa 80% na mabiyanta a Kwara
“Har yau ba mu ga inda ake yi wa ‘ya ‘yan jam’iyya rajista a Kwara ba, amma kuma an bada sanarwar kara wa’adin yin rajista, ba tare da an kawo takardun aiki ba."
Jigon na APC ya yi ikirarin kusan 80% na ‘ya ‘yan jam’iyya za su iya barin APC domin suna tare da bangarensu, don haka ya ja-kunnen Mai Mala Buni su dinke barakar.
A bangaren jam'iyyar hamayya kuwa, PDP ta yi wa APC albishir, ta fadi lokacin da kusoshinta za su tsere daga Jam’iyyar saboda rikicin cikin gidan da zai barko mata.
Jigon PDP, Diran Odeyami ya bayyana cewa Gwamnoni da Sanatoci za su fice daga jam'iyyar APC da zarar an yi zaben shugabanni saboda rashin jituwa da za a samu.
Asali: Legit.ng