Zargin cin amana: Jam’iyyar PDP ta dakatar da babban jigonta a wata jihar Arewa

Zargin cin amana: Jam’iyyar PDP ta dakatar da babban jigonta a wata jihar Arewa

  • PDP ta dakatar da tsohon dan takarar gwamnan jihar Neja a karkashin inuwar jam'iyyar, Alhaji Umar Nasko
  • PDP a karamar hukumar Magama ta zargi Nasko da wasu ayyuka da ya sabawa jam’iyyar
  • An tattaro cewa tsohon dan takarar gwamnan ya taimaka wa dan takarar APGA a zaben cike gurbi da aka yi da kudade da motocin yakin neman zabe

Minna, Jihar Neja- An dakatar da tsohon dan takarar gwamnan jihar Neja a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Umar Nasko saboda wasu ayyuka da ya sabawa jam’iyyar.

Ana zargin Nasko da daukar nauyi da kuma taimaka wa dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a zaben fidda gwani na dan takarar kujerar mazabar tarayya ta Magama/ Rijau da kudi da motocin yakin neman zabe.

Ana zargin shi ma ya yi yakin neman zaben sannan kuma ya umarci dukkan magoya bayansa da su zabi dan takarar APGA a kan dan takarar PDP, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan daba suka kai masa farmaki

Zargin cin amana: Jam’iyyar PDP ta dakatar da babban jigonta a wata jihar Arewa
Jam’iyyar PDP ta dakatar da tsohon dan takararta na gwamna a jihar Neja Hoto: The Nation
Asali: UGC

Dakatarwar da zargin sun kasance a cikin wata wasika da suka aika wa jam’iyyar PDP reshen Neja mai taken, ‘Sanarwar dakatar da Umar Muhammed Nasko daga PDP, karamar hukumar Magama, jihar Neja’.

Wasikar mai dauke da kwanan wata 23 ga watan Yuli, yana dauke da sa hannun shugaban PDP a karamar hukumar, Aminu Mohammed da mataimakin Sakataren jam’iyyar, Tasiu Musa.

A cewar wasikar, dakatarwar na daga cikin hukuncin da aka gabatar kuma aka zartar a yayin taron gaggawa na jam'iyyar, Naija News ta ruwaito.

Wasikar ta ce:

“An dakatar da tsohon dan takarar gwamna a jihar Neja, Alhaji Umar Muhammed Nasko daga jam’iyyar a karamar hukumar Magama.
"Zarge-zargen da ake yi masa sun kasance masu karfi na ayyukan adawa da jam'iyyar a zaben cike gurbi da aka kammala na Mazabar Magama / Rijau ta Tarayya inda ya yi kamfen tare da umartar dukkan magoya bayansa da su zabi dan takarar APGA a kan dan takarar PDP kuma ya taimaka wa dan takarar APGA da kudade da motocin yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

“Ya ki halartar tarurrukan jam’iyya da harkoki a Karamar Hukumar Magama. Ya kasance yana tunzura mambobi a tsakaninsu da haifar da matsala da rashin yarda wanda ya sa sauran mambobin jam'iyyar ficewa zuwa wasu jam'iyyun siyasa.
“Misalin shi ne irin adawa da yake yi da shugaban karamar hukuma wanda ya yi gwagwarmaya dashi har sai da aka tilasta wa Shugaban sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta APC.
“Ya kasance yana tunzura mambobi a kan shugaban babbar jam’iyyarmu (PDP) a jihar Neja, Dr Mu’azu Babangida Aliyu, wanda ya raina kuma ba ya ba shi girmamawar da ya kamata a matsayinsa na tsohon gwamna kuma shugaban jam’iyyar a jihar.”

Babangida: PDP ta amince da dakatarwar da aka yi wa daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya a Arewa

A wani labarin, jam’iyyar PDP ta reshen jihar Neja, ta tabbatar da cewa Mu’azu Babangida Aliyu ya na nan a matsayin wanda aka dakatar.

Kara karanta wannan

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana da manya kan batun

Jam’iyyar PDP ta ce an dakatar da tsohon gwamna, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu saboda rawan da ya taka wajen juya wa Goodluck Jonathan baya a 2015.

Rahoton ya ce PDP ta fito, ta bada wannan sanarwa ta bakin mai magana da yawun bakinta a mazabar tsohon gwamnan, Malam Yahaya Mohammed Usman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel