Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana da manya kan batun

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana da manya kan batun

  • Wani matashi daga jihar Kano ya gana da makusanta Ganduje domin sanar dasu aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa
  • Matashin ya bayyana balo-balo cewa, zai tsaya takarar shugaban a karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaben 2023
  • Sai dai, wasu matasan sun bayyana goyon bayansu ga gwamnan jihar Bauchi, inda suke neman shi ma ya tsayawa takarar

Wani matashi dan shekaru 35 da ke neman tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC a jihar Kano, Malam Aminu Sa’idu, a jiya ya gana da mataimaka na musamman (SAs) ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje don sanar da su burinsa.

Da yake magana da Daily Trust bayan ganawar, matashin ya ce yana daga cikin shawarwarin da yake bi gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Ya kuma ce ganawar ta yi daidai da kudirin dake rajin ba matasa damar a dama dasu a mulki na"Not Too Young to Run", da kuma dabarun fadada aniyarsa zuwa dukkan sassan kasar.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

KARANTA WANNAN: Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Taswrirar jihar Kano | Hoto: vanguardngr.com
Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana manya kan batun
Asali: UGC

Wata kungiya ta yi kira da a mika Najeriya ga gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed

Amma wata kungiyar matasan Arewa a karkashin inuwar kungiyar Concerned Citizens Like-Minds (CCLM) ta ce Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ne mafi cancanta wajen tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, jaridar Sun ta ruwaito.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a Kaduna, kakakin kungiyar, Kwamared Mujaheed Amin-Modibbo, ya ce:

“Sanata Bala ya nuna halaye na kwarai na nagartaccen shugaba tun lokacin da ya fara siyasa a Najeriya tun daga asalinsa, a matsayin minister a FCT sannan a matsayin Gwamna na yanzu na jihar Bauchi.”

Kungiyar ta nemi gwamnan ya tsaya takarar shugaban kasa; yakin neman zabe da karfi, lashe zaben tare "dawo da" martabar kasar.

Kara karanta wannan

Kotun Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Matawalle saboda sauya sheka zuwa APC

KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Shirin Sallah: Wani gwamna ya biya ma'aikata albashi, ya rabawa gajiyayyu kudade

A wani labarin, a ci gaba da shirye-shiryen babbar sallah mai zuwa, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya amince da biyan dukkan albashin watan Yuli nan take ga dukkan ma'aikatan gwamnati a fadin jihar.

Hakazalika gwamna Zulum ya fitar da sama da N100m don rabawa bangarori daban-daban na Mutanen da ke fama da nakasa (PLWDs).

Sama da Naira N100m ga masu karamin karfi a matsayin wani bangare na abinda Gwamnati mai ci yanzu ta kirkiro, wanda galibi Kwamishinan Wasanni da Ci gaban Matasa, Hon Saina Buba ke rabawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel