Tsohon kwamishina ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan daba suka kai masa farmaki

Tsohon kwamishina ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan daba suka kai masa farmaki

  • 'Yan daba da ake zargin magoya bayan Obasa ne sun kaiwa tsohon kwamishina a jihar Legas farmaki
  • An gano cewa 'yan daban sun kaiwa Kayode Opeifa farmaki har gidansa dake Agege a ranar Lahadi da ta gabata
  • Sun samu hargitsi da Obasa ne bayan magoya bayansa sun koma goyon bayan dan takarar YPP a zaben kananan hukumomi

Agege, Legas

'Yan daba da ake zargin magoya bayan kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Oabasa sun kaiwa tsohon kwamishinan sufuri na jihar, Kayode Opeifa farmaki.

SaharaReporters ta tattaro cewa an kaiwa Opeifa farmaki a gidansa dake titin Oyewole dake tashar motan Mulero, Agege, a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane a Abuja sun fara karbar kudin fansa ta banki

Tsohon kwamishina ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan daba suka kai masa farmaki
Tsohon kwamishina ya tsallake rijiya da baya yayin da 'yan daba suka kai masa farmaki. Hoto daga saharareporters.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu

Me ya hada Obasa da tsohon kwamishinan?

Wata majiya wacce ta ga lokacin da aka kai farmakin, ta ce 'yan daban sun je kalubalantar kwamishinan kan zarginsa da ake yi da kaka gida ga masu zabe a gunduma ta D, karamar hukumar hukumar Agege.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

Majiyar ta ce:

Wasu mambobin jam'iyyar APC a gundumar da suka samu jagorancin Obasa sun yi watsi da dan takarar Adeoye inda suka koma goyon bayan dan takarar YPP, Afolabi Omotunde.
A ranar Asabar, a bayyane suka nuna goyon bayansu ga dan takarar YPP kuma tawagarsa ta tsananta tare da matsawa domin hakan magudin zabe.
A yammacin ranar Lahadi, 'yan daban dake goyon bayan dan takarar YPP sun tsare jama'ar Oyewole inda suka dinga kai musu farmaki. Sun taru a gaban gidansa amma daga bisani sun tafi. Sun koma wurin karfe 3 na dare kuma sun kai masa farmaki har gida. Sun dinga harbe-harbe tare da jifa da duwatsu tare da sauran miyagun makamai.

Jigon jam'iyyar APC ya yi Allah wadai da al'amarin

Kamar yadda SaharaReporters ta tattaro, wani jigon jam'iyyar APC yayi Allah wadai da wannan al'amarin inda ya kwatanta shi da ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar baki daya.

Kara karanta wannan

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana da manya kan batun

Jigon APC yace wannan salon siyasar da aka kirkiro a karamar hukumar Agege abun tsoro ce da firgici, don haka dole ne jam'iyyar ta zabura tare da magance babbar matsalar nan

A wani labari na daban, gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar PDP sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da mayar da fadar shugaban kasa zuwa sakateriyar APC, Daily Trust ta ruwaito.

A wani taro da suka yi a jihar Bauchi, gwamnonin PDP sun ce fadar shugaban kasa ta kowanne dan Najeriya ce amma an mayar da ita hedkwatar PDP inda ake ganin 'yan PDP da aka tirsasa zuwa APC akai-akai.

Gwamnonin sun kara da kushe yadda ake amfani da wasu irin dabaru domin janye wasu daga cikin gwamnonin PDP inda ake tirsasa su zuwa jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel