Dakarun Sojoji sun kama ‘Yan fasa-kauri za su tsallako da buhuna 160 na shinkafa ta teku

Dakarun Sojoji sun kama ‘Yan fasa-kauri za su tsallako da buhuna 160 na shinkafa ta teku

  • Sojojin ruwan Najeriya sun kama wani jirgin ruwa ya dauko buhunan shinkafa
  • Commodore Bashir Mohammed ya bada wannan sanarwar a ranar Lahadin nan
  • An mika wannan jirgi da ya dauko kayan fasa-kauri zuwa ga jami’an Kwastam

Yayin da yake shawagi, jirgin sojojin ruwan Najeriya na BEECROFT wanda aka fi sani da NNS, ya yi yi kici bis da wasu shinkafa da ake kokarin a shigo da su.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa wannan jirgi na sojoji ya samu wani jirgin ruwa na katako ya dauko buhuna 162 na shinkafar kasar waje kan ruwan Legas.

Jami’an sojojin ruwan Najeriya sun fitar da jawabi ta bakin Commodore Bashir Mohammed a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuli, 2021, suka bayyana wannan.

KU KARANTA: Yadda Gwamna ya ba Buhari miliyoyin gaf da zabe, amma ya ki karba

Commodore Bashir Mohammed ya ce an kama wannan jirgin ne a ranar 8 ga watan Yuli, 2021, da kimanin karfe 3:30 na yamma ya dauko wadannan tulin kaya.

Kara karanta wannan

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

“Bincike ya soma nuna mana cewa an jigilo shinkafan ne daga kasar Benin, za a shigo da su Najeriya a sace. Duka shinkafan na kasar waje ne.”
“Kamar yadda sojojin ruwa suka saba aiki, a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuli, 2021, jirgin NNS BEECROFT ya mika wannan jirgi na Cotonou da buhuna 162 na shinkafa ga jami’an da ke hana fasa-kauri”

Commodore Mohammed ya gargadi masu shigo da kaya a sace, su yi hattara da bi ta ruwan Legas.

Dakarun Sojoji sun kama ‘Yan fasa-kauri za su tsallako da buhuna 160 na shinkafa ta teku
Jirgin sojojin ruwa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ba zai yiwu mu rage farashin buhun shinkafa ba - 'Yan kasuwa

Babban jami’in ya ce sojojin ruwan Najeriya za suyi kokarin kawo karshen fasa-kauri a yankin, kamar yaddda Hafsu Vice Admiral Awwal Gambo ya bada umarni.

Sojojin ruwa suna kokarin ganin an kawo karshen masu fasa-kauri tsakanin 2021 zuwa shekarar 2025.

Today.ng ta ce a madadin hafsun sojojin ruwa na kasa, Awwal Gambo, Commodore Mohammed ya yi kira ga jama’a su bas u hadin-kai wajen tona wa masu laifi asiri.

Kara karanta wannan

NAF: Rundunar sojin sama ta magantu kan labarin sabon hatsarin jirgin sama a Kaduna

A makon da ya gabata ne ku ka ji cewa duk wanda aka samu ya yi garkuwa da mutane, ko ya taimaka wajen yin hakan, zai bakunci lahira ta hanyar rataya a Neja.

Za a rika hallaka masu satar Bayin Allah da dabbobi, da masu taimaka masa da bayanai. Gwammna Abubakar Sani Bello ya ce hakan zai kawo zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng