Labari mai zafi: Hatsarin mota ya hallaka mutane da dama a hanyar zuwa Minna

Labari mai zafi: Hatsarin mota ya hallaka mutane da dama a hanyar zuwa Minna

  • Hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane 7 a kan hanyar Lambata zuwa Minna
  • Hatsarin ya faru da safiyar yau Alhamis, 22 ga watan Yuli mintoci kadan bayan karfe bakawai
  • An ruwaito cewa, ganganci da gudun wuce gona da iri na direbobin ne ya jawo mummunan hatsarin

Mutum bakwai sun mutu, a safiyar ranar Alhamis, a wani mummunan hatsarin mota wanda ya faru a hanyar Lambata zuwa Minna, jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Hatsarin, a cewar kwamandan sashin kula da hadurra (FRSC), Musa Muhammed, ya faru ne a kauyen Dagibe 'yan mintoci kadan bayan karfe 7 na safe.

Hatsarin ya rutsa da motoci biyu, wata mota kirar Mazda 323 mai lamba kamar haka CRC686XN da kuma wata motar golf ta Volkswagen mai lamba KTU506BK.

Jami’an hukumar FRSC ba su iya tantance ko su wanene wadanda lamarin ya rutsa da su ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton amma maza shida da mace daya sun mutu.

Labari mai zafi: Hatsarin mota ya hallaka mutane 7 a hanyar zuwa Minna
Lokacin da aka yi hatsarin | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wannan mummunan hatsarin ya yi sanadin raunata maza biyu.

Bayanai sun ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudu na wuce gona da iri da kuma rashin kulawar da direbobin ke yi.

Wadanda suka jikkata, a cewar Muhammed, an kai su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Gawu Babangida yayin da aka kai gawarwakin dakin ajiyar gawarwakin na Sabon Wuse.

Jirgin saman sojojin sama na Najeriya ya sake hadari a Kaduna, jami'an ceto sun kai dauki

Babu wani labari game da halin da ma'aikatan jirgin dake cikin jirgin ke ciki a lokacin hada wannan rahoton.

Rahoto da muke samun ya shaida cewa, jirgin saman sojin sama na Najeriya ya yi hadari a cikin jihar Kaduna.

Jirgin mai suna AlfaJet an ce ya bar Yola babban birnin jihar Adamawa ne don ayyukan yaki da ta'addanci wanda kwatsam ya fadi a daya daga cikin kauyukan yankin jihar ta Kaduna.

Wani babban jami’in NAF da bai so a ambaci sunansa a rubuce ba, ya fadawa jaridar Daily Sun cewa sansanin NAF din da ke Yola tuni ya shiga bakin ciki da jimami lokacin da labarin hadarin ya iso su.

A wani labarin, akalla jami'an Kwastam uku da wani soja sun ji rauni lokacin da wasu masu fasa kwauri suka far musu a yankin Igboora da ke karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo a ranar Juma'a.

Theophilus Duniya, Jami’in Hulda da Jama’a na Kwastam, sashin Ayyuka na Tarayya, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar kuma ya ba manema labarai a Ibadan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel