Barka da Sallah: Shugaba Buhari Ya Gwangwaje Yan Bautar Kasa NYSC da Kyautar Kudi da Shanu a Daura

Barka da Sallah: Shugaba Buhari Ya Gwangwaje Yan Bautar Kasa NYSC da Kyautar Kudi da Shanu a Daura

  • Shugaba Buhari ya baiwa matasa yan bautar ƙasa dake aiki a Daura kyautar kuɗi, shanu da buhunan shinkafa
  • Buhari ya nuna jin daɗinsa da ziyarar barka da sallah da matasan suka kai masa har gida, ya kuma roke su da su zama jakadu nagari
  • Shugaban NYSC na jihar Katsina, Alhaji Yahaya, ya godewa shugaban da irin wannan kyauta da ya saba yi

A ranar Talata, Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya baiwa matasa yan bautar ƙasa (NYSC) waɗanda suke aiki a ƙaramar hukumar Daura, jihar Katsina, kyautar kuɗi naira miliyan ɗaya (N1m) da shanu guda biyu, da kuma buhunan shinkafa 20, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Jirgin Yakin Sojojin Sama NAF da Ya Fado a Zamfara

Kakakin NYSC reshen jihar Katsina, Mr. Alex Obemeata, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Talata.

Yace shugaba Buhari ya ba su wannan kyautar ne yayin da suka kai masa ziyarar barka da sallah a gidansa dake Daura, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Buhari ba baiwa yan bautar ƙasa Shanu biyu
Barka da Sallah: Shugaba Buhari Ya Gwangwaje Yan Bautar Kasa NYSC da Kyautar Kudi da Shanu a Daura Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yace: "Wata sallah ce mai cike da farin ciki ga matasan NYSC dake aiki a Daura, mahaifar shugaban ƙasa Buhari, domin sun yi shagalin sallah tare da shi."

"Kamar yadda aka saba, idan Buhari ya zo gida hutun sallah, matasan NYSC suna kai masa ziyarar barka da zuwa, kuma su masa barka da sallah."

"A ranar 20 ga watan Yuli, yan bautar ƙasa sun kaiwa shugaban ziyara da masa fatan an yi sallah lafiya. A wannan ziyara an basu shanu biyu, buhunan shinkafa 20 da kuma kuɗi miliyan N1m."

Buhari ya yabawa matasan NYSC

Kakakin NYSC ya ƙara da cewa shugaba Buhari ya yabawa matasan, sannan ya roƙe su da su zama jakadu nagari, kuma su yi aiki domin cigaban ƙasa.

A cewar Obemeata, shugaban NYSC na jihar Katsina, Alhaji Ahidjo Yahaya, ya godewa shugaban bisa wannan abin alkairi a madadin Darakta na ƙasa, Janar Shua'aibu Ibrahim.

KARANTA ANAN: Masarauta a Jihar Kano Ta Dakatad Da Wani Basarake Saboda Zargi

Ya bayyana cewa irin wannan abun da shugaba Buhari ya saba yi zai ƙara wa yan Najeriya kwarin guiwa wajen haɗin kan kasa ba tare da nuna banbanci ba, wanda aka kafa NYSC domin haka kuma take aiwatarwa.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Kwararren Likita a Jihar Kogi

Yan bindiga sun yi awon gaba da likita a asibitin Ugwolawo ƙaramar hukumar Ofu, jihar Kogi , mai suna Solomon Nidiamaka.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun tilastawa likitan tafiya da su ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a harabar asibitin ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel