Masarauta a Jihar Kano Ta Dakatad Da Wani Basarake Saboda Zargi

Masarauta a Jihar Kano Ta Dakatad Da Wani Basarake Saboda Zargi

  • Masarautar Karaye dake jihar Kano ta dakatad da magajin garin ƙauyen Butu-Butu saboda wani zargi
  • Hakimin Rimin Gado, Alhaji Tukur, shine ya kai korafin basaraken kan zargin haddasa fitina tsakanin mutane
  • Sarkin Karaye, Ibrahim Abubakar II, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin

Majalisar masarautar Ƙaraye dake jihar Kano ta dakatad da magajin garin Butu-butu dake ƙaramar hukumar Rimin Gado, Abdullahi Sa'adu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Kwararren Likita a Jihar Kogi

Dakatad da Sa'adu ta biyo bayan ƙorafinsa da Hakimin Rimin Gado, Alhaji Auwalu Ahmed Tukur, ya shigar, inda yake zarginsa da aikaita ba dai-dai ba.

Ana zargin magajin garin da hannu a siyar da filaye ba bisa ƙa'ida ba ga fulani makiyaya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Hakanan kuma ana zarginsa da jagorantar ginin wani masallaci ba tare da bin matakan da ya kamata ba wanda hakan ya jawo rikici da rarrabuwar kai tsakanin mutanensa.

Kara karanta wannan

Kano: An sauke shugaban makaranta saboda ya bai wa dalibai hutun Sallah

Masarautar Karaye ta dakatad da magajin garin Butu-Butu
Masarauta a Jihar Kano Ta Dakatad Da Wani Basarake Saboda Zargi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Masarauta zata yi bincike

A wani jawabi da kakakin masarautar Ƙaraye, Haruna Gunduwawa, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa an dakatar da shi ne domin baiwa kwamitin da aka kafa damar gudanar da bincike yadda ya kamata game da zargin da ake masa.

"An dakatar da shi ne domin baiwa masu bincike damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata." inji shi.

Sarkin Ƙaraye, Ibrahim Abubakar II, ya umarci Shehu Ahmed, babban ɗan majalisar masarauta, da ya gudanar da bincike kan lamarin.

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane da Dama a Kauyukan Jihar Benuwai

Hakanan masarautar ta tura madakin Shamaki, Malam Habibu Umar, domin kula da yankin Butu-Butu yayin da ake bincike.

A wani labarin kuma Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci yan Najeriya da su ƙara hakuri da gwamnatinsa, domin nan ba da jimawa ba zasu samu walwala.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

Shugaban ya taya ɗaukanin yan Najeriya murnar zagayowar babbar sallah (eid-el-kabir) tare da fatan Allah ya maimaita mana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262