Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Jirgin Yakin Sojojin Sama NAF da Ya Fado a Zamfara

Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Jirgin Yakin Sojojin Sama NAF da Ya Fado a Zamfara

  • Shugaban ƙasa, Buhari, ya nuna rashin jin daɗinsa da hatsarin jirgin yaƙin NAF a jihar Zamfara
  • Buhari, wanda aka bashi labarin lamarin da ya faru a mahaifarsa Daura, yace ya kaɗu sosai da jin labarin
  • Shugaban ya yi fatan samun lafiya cikin sauri ga matuƙin jirgin, wanda ya tsira da rayuwarsa

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yabawa matuƙin jirgin yaƙin rundunar sojin sama (NAF). Abayomi Dairo, wanda ya tsira da rayuwarsa yayin wani operation a Zamfara ranar Lahadi.

KARANTA ANAN: Masarauta a Jihar Kano Ta Dakatad Da Wani Basarake Saboda Zargi

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindiga ne suka kakkaɓo jirgin yaƙin NAF, amma matuƙin jirgin ya tsira.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar a shafinsa na Facebook.

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Jirgin Yakin Sojojin Sama NAF da Ya Fado a Zamfara Hoto: @BashirAhmad
Asali: Instagram

Wani sashin jawabin yace:

"Shugaba Buhari ya yabawa gwarzon matuƙin jirgin yaƙin NAF, Lieutenant Abayomi Dairo, wanda ya tsira da rayuwarsa daga jirgin da ya faɗo ba shiri sabida matsin yan bindiga a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

"Shugaban wanda aka yi masa bayani dangane da nasarar da jami'an tsaron ƙasar nan suka samu wajen kuɓutar da matuƙin jirgin, ya bayyana cewa ya kaɗu da jin labarin."

Banji daɗin abunda ya faru ba-Buhari

Shugaba Buhari ya nuna rashin jin daɗinsa kan labarin kaɓo jirgin yaƙin NAF, ya kuma yi wa matuƙin addu'ar fatan samun lafiya cikin gaggawa.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Kwararren Likita a Jihar Kogi

Buhari, yace: "Na kaɗu matuka da jin labarin hatsarin jirgin, amma kuma naji daɗi da a ka faɗa mun matuƙin jirgin ya tsira."

"Ina addu'a Allah ya bashi lafiya, ya warke daga raunukan da ya samu yayin hatsarin."

A wani labarin kuma Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane da Dama a Kauyukan Jihar Benuwai

Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayuwarsu a wasu ƙauyukan dake ƙaramar hukumar Guma, jihar Benuwai.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Nasarar Shugaba Buhari Nasarar Ku Ce, COS Ga Yan Najeriya

Wani shaida ya bayyana cewa an aikata kisan ne a wurare daban-daban ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Guma, harda masu bada agajin gaggawa biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel