Da Dumi-Dumi: DSS Ta Hana Nnamdi Kanu Sanya Hannu a Takardar Taimakon Burtaniya

Da Dumi-Dumi: DSS Ta Hana Nnamdi Kanu Sanya Hannu a Takardar Taimakon Burtaniya

  • Hukumar DSS ta hana Nnamdi Kanu ya sanya hannu a takardar da Burtaniya ta aiko masa
  • Ɗaya daga cikin lauyoyin shugaban tawaren, Aloy Ejimakor, shine ya bayyana haka ranar Litinin
  • Tun bayan sake kama Kanu da gwamnati ta yi, an cigaba da tsare shi a hannun jami'an DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta hana tsararren shugaban ƙungiyar tawaren IPOB, Nnamdi Kanu, ya sanya hannu akan takardar taimako da Burtaniya ta aiko masa, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Cutar COVID19: NAFDAC Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ba Ta Amince da Magungunan Gargajiya Ba

Ɗaya daga cikin lauyoyin shugaban IPOB ɗin, Aloy Ejimakor, shine ya bayyana haka a wani jawabi da yayi jim kaɗan bayan yakai masa ziyara ranar Litinin.

Shugaban tawaren IPOB, Kanu, yana da takardar fasfo ɗake shaidar zama cikakken ɗan ƙasa a Najeriya da Burtaniya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

Nnamdi Kanu
Da Dumi-Dumi: DSS Ta Hana Nnamdi Kanu Sanya Hannu a Takardar Taimakon Burtaniya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Lauyan yace: "Ranar Asabar da na ziyarci Kanu, banji daɗi ba da naga bai sanya hannu a takardin da na kai masa ba. Na kaiwa DSS takardun biyu domin su bashi dama ya sanya hannu."

"Takardun suna da alaƙa da taimakon da ƙasar Burtaniya takeson ba shi, ta ofishin jakadancinta dake Najeriya."

"Abun mamakin shine an dawo mun da takardon ba tare da sanya hannun da na buƙata ba."

An Sake kamo Kanu a ƙasar waje

Kanu, wanda gwamnati da sake damƙe wa kwanan nan a ƙasar waje, yana fuskantar tuhumar ta'addanci a gaban alƙali yayin da ya tsallake ya tsere bayan baɗa belinshi.

Sai dai gwamnati ta sake kamo shi, ta dawo da shi Najeriya, tun daga wannan lokaci yake tsare a hannun jami'an hukumar DSS.

KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Nasarar Shugaba Buhari Nasarar Ku Ce, COS Ga Yan Najeriya

A wani labarin kuma Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane da Dama a Kauyukan Jihar Benuwai

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Nasarar Shugaba Buhari Nasarar Ku Ce, COS Ga Yan Najeriya

Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayuwarsu a ƙauyuka daban-daban na jihar Benuwai.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutanen ne a ƙauyuka uku dake ƙaramar hukumar Guma.

Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a shekarar 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya yi karanci Lissafi a digirinsa na farko a jami'ar kimiyya da fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel