Babbar Sallah: Nasarar Shugaba Buhari Nasarar Ku Ce, COS Ga Yan Najeriya

Babbar Sallah: Nasarar Shugaba Buhari Nasarar Ku Ce, COS Ga Yan Najeriya

  • Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Ibrahim Gambari, ya roƙi yan Najeriya su baiwa gwamnatin Buhari goyon baya
  • COS Gambari ya yi wannan kira ne yayin da ya isa mahaifarsa Ilorin a karon farko tun bayan naɗinsa
  • Manyan jiga-jigan gwamnatin Kwara, Sanatoci da sauran al'umma ne suka yi dandazo wajen tarbar Gambari

Shugaban ma'aikata na fadar shugaban ƙasa, Ibrahim Gambari, ya roƙi yan Najeriya su baiwa shugaba Buhari dukan goyon bayan da ya kamata, inda yace: "Nasarar shugaba Buhari nasarar mu ce, mu yan Najeriya" kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gwamna Ya Caccaki Sanatocin APC, Ya Fadi Munafuncin da Suke Shiryawa a Zaben 2023

Gambari ya ziyarci mahaifarsa, Ilori, a karon farko tun bayan naɗa shi, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa (COS).

Kuma yayi wannan kira ne yayin fira da manema labarai a Birnin Ilorin, babbar birnin jihar Kwara.

COS Ibrahim Gambari
Nasarar Shugaba Buhari Nasarar Ku Ce, COS Ya Faɗawa Yan Najeriya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

COS Gambari yace: "Wanna lokacin (babbar sallah) wata dama ce da zamu nuna ƙauna ga ƙasar mu, kuma mu cigaba da goyon bayan shugaba Buhari saboda nasararshi ta mu ce."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

"Da izinin Allah duk wasu shirye-shiryen da gwamnati ta ƙirƙiro da ayyukan da ta fara a ɓangaren tattalin arziƙi, siyasa, da jin ƙai da walwala zasu tabbatar da inganta rayuwar yan Najeriya."

"Zuwa ƙarshen mulkin shugaba Buhari, Najeriya zata ƙara dunƙulewa ƙasa ɗaya, kuma za'a ƙara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali."

Jiga-jigan gwamnati sun tarbi Gambari

Manyan jiga-jigan gwamnatin jihar Kwara bisa jagorancin mataimakin gwamna, Mr. Kayode Alabi, sune suka tarbi COS Gambari a filin tashi da saukar jiragen sama dake Ilorin, kamar yadda leadership ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Sako Sarki Mai Daraja Ta Daya da Suka Sace a Kogi

Sauran waɗanda suka tarbi COS ɗin sun haɗa da, Sanatocin dake wakiltar Kwara ta tsakiya da ta arewa, Ibrahim Oloriegbe da Sadiq Umar, kakakin majalisar dokokin jihar, Yakubu Danladi Salihu, da kuma mai baiwa gwamna shawara kan al'amuran siyasa, Abdullateef Alakawa.

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga da Dama Yayin Wani Artabu a Neja

Hakazalika manyan jiga-jigan jam'iyyar APC da ɗumbin jama'a masoya sun je filin jirgin domin tarbar COS Ibrahim Gambari.

A wani labarin kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga da Dama Yayin Wani Artabu a Neja

Gwarazan yan sanda a jihar Neja sun hallaka yan bindiga akalla 10 a wani gumurzu da suka yi.

An fafata tsakanin yan sandan da maharan, inda suka samu nasarar fatattakar su daga kai hari ƙauyen Kundu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel