Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Kwararren Likita a Jihar Kogi

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Kwararren Likita a Jihar Kogi

  • Wasu yan bindiga sun sace wani ƙwararren likita a harabar asibitin da yake aiki a jihar Kogi
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun tilastawa likitan tafiya da su da safiyar Litinin
  • Ƙungiyar likitoci reshen jihar ta tabbatar da sace likitan a wani saƙo da ta fitar

Yan bindiga sun yi awon gaba da likita a asibitin Ugwolawo ƙaramar hukumar Ofu, jihar Kogi, mai suna Solomon Nidiamaka, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane da Dama a Kauyukan Jihar Benuwai

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun tilastawa likitan tafiya da su ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a harabar asibitin ranar Litinin.

A wani jawabi da ƙungiyar likitoci (NMA) reshen jihar ta fitar ɗauke da sanya hannun shugabanta, Dr Omakoji Oyiguh, da sakatare, Dr Famotele Talorunju, ta tabbatar da sace likitan.

Yan bindiga sun sace likita a Kogi
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Kwararren Likita a Jihar Kogi Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani ɓangaren jawabin yace:

"Ƙungiyar likitoci na sanar wa mutane cewa an yi awon gaba da mambanta, Dr. Solomon Nidiamaka, dake aiki a asibitin Ugwolawo ƙaramar hukumar Ofu da misalin ƙarfe 8:30 na safe a harabar asibitin."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

"Muna kira ga gwamnatin jihar Kogi da hukumomin tsaro da su matsa sosai wajen ganin sun ƙuɓuyar da shi cikin gaggawa."

KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

Yan sanda ba su da labari

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kogi, Mr. William Aya, ya bayyana cewa hukumar yan sanda batasan da faruwar lamarin ba.

Sai dai yayi alƙawarin sanarwa a hukumance da zarar ya samu rahoto daga DPO dake kula da yankin.

A wani labarin kuma DSS Ta Hana Nnamdi Kanu Sanya Hannu a Takardar Taimakon Burtaniya

Hukumar DSS ta hana Nnamdi Kanu ya sanya hannu a takardar da Burtaniya ta aiko masa.

Daya daga cikin lauyoyin shugaban tawaren, Aloy Ejimakor, shine ya bayyana haka ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262