Jerin manyan hukumomin gwamnati da ke daukar ma’aikata a yanzu haka

Jerin manyan hukumomin gwamnati da ke daukar ma’aikata a yanzu haka

Ga ‘yan Najeriya masu neman aikin yi, a kalla hukumomin gwamnati uku suna daukar ma’aikata a halin yanzu yayin da suke neman karin hannaye don tafiyar da ayyukansu.

KU KARANTA KUMA: 2023: Abubakar Yar’adua ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar kujerar gwamnan Katsina

Ga jerin hukumomin gwamnati guda uku da ke saukar ma’aikata a yanzu haka:

Jerin manyan hukumomin gwamnati da ke daukar ma’aikata a yanzu haka
Manyan hukumomin gwamnati na daukar ma’aikata a yanzu haka Hoto: Nigerian Air Force HQ, HQ Nigerian Army, Federal Road Safety Corps Nigeria
Asali: Facebook

Rundunar Sojin Sama

Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) tana daukar daliban da suka kammala karatun digiri da digiri na biyu don samun horo a matsayin hafsoshin Cadets.

Za a bude shafin yanar gizo na neman aikin a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, sannan za a kulle a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta. Karanta abubuwan da ake bukata a nan.

Rundunar sojojin Najeriya

Rundunar Sojojin Najeriya ma ta fitar da jerin cibiyoyin daukar ma’aikata a cikin jihohi 36 na tarayyar kasar da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) don daukar ma'aikata 81 kamar yadda ta saba.

Kara karanta wannan

Bayani dalla-dalla: Yadda ake za ka nemi aiki a hukumomin Gwamnatin Tarayya uku da ke daukar aiki a yanzu

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, an fara daukar ma’aikatan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, kuma za a rufe a ranar Asabar, 24 ga watan Yuli.

Danna nan don ganin jerin cibiyoyin daukar ma'aikata.

KU KARANTA KUMA: Kano: An sauke shugaban makaranta saboda ya bai wa dalibai hutun Sallah

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC)

Hakanan, yan Najeriya masu neman yin aiki tare da gwamnatin tarayya zasu iya samun damar yin hakan a yanzu kamar yadda Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa ta sanar da daukar aikinta na 2021.

Hukumar kiyaye hadurra ta ce “wadanda suka cancanta” na iya neman aikin a wadannan mukamai:

  • Officer cadre
  • Marshal inspectorate (MI) cadre
  • Road marshal assistant cadre

A cewar sanarwar daukar ma'aikata da aka wallafa a shafin Facebook, ana sa ran masu neman mukamin officer cadre su mallaki digiri na farko, takardar shaidar kammala NYSC, kuma dole ne su kasance ba su wuce shekaru 30 ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba a matsayin hutu

A wani labarin, dakarun sojin Najeriya sun sheke wasu mutum uku da ake zargin 'yan Boko Haram ne tare da damke wasu 11 a cikin kokarin kawo karshen ta'addanci da suke yi a yankin arewa maso gabas.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasan, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce an sun fatattaki 'yan ta'addan wurin Banki kan babban titin Miyanti inda suka hana 'yan ta'addan wucewa tare da miyagun makamansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng