Kano: An sauke shugaban makaranta saboda ya bai wa dalibai hutun Sallah

Kano: An sauke shugaban makaranta saboda ya bai wa dalibai hutun Sallah

  • An dakatar da Shugaban Makarantar GSS Dambatta, Sabo Muhammad Ahmad daga mukaminsa
  • Hakan ya biyo bayan take umurnin gwamnatin jihar Kano da Sabo ya yi wajen bai wa daliban da ke rubuta jarrabawar NECO hutun babban Sallah
  • Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Sanusi Sa'id Kiru ya kuma umarci shugaban makarantar da ya gabatar da kansa a Ma’aikatar Ilimin

Wani rahoton jaridar Aminiya ya nuna cewa kwamishinan ilimi na Jihar Kano, Sanusi Sa’id Kiru, ya amince da sauke Shugaban Makarantar GSS Dambatta, Sabo Muhammad Ahmad daga mukaminsa.

An tattaro cewa wannan matakin ya biyo bayan saba wa umarnin gwamnatin jihar da Shugaban makarantar yayi wajen bai wa dalibai hutun Babbar Sallah.

KU KARANTA KUMA: 2023: Abubakar Yar’adua ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar kujerar gwamnan Katsina

Kano: An sauke shugaban makaranta saboda ya bai wa dalibai hutun Sallah
Shugaban makarantar ya bai wa daliban da ke zana jarrabawar NECO hutun Sallah Hoto: EduCeleb
Asali: UGC

Bayanai sun ce an sauke shi ne sakamakon bayar da hutun ga dalibai 300 da ke zana jarrabawar kammala sakandire ta NECO.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa farashin kayan Masarufi yayi tashin gwauron zabi, Shugaba Buhari

Aminiya ta kuma kawo cewa, hakan ya saba da umarnin da gwamnatin Jihar ta bayar na ci gaba da tabbatar da zaman daliban a wannan lokaci.

A cewar Kwamishinan Ilimin, Sabo Muhammad ya bai wa daliban damar koma wa gidajensu, inda shi ma ya koma garinsa domin gudanar da bikin Sallah ba tare da sanar wa mahukuntan da suka dace ba.

Kiru ya ce:

“Wannan lamari ya nuna sakaci da halin-ko-in–kula gami da cin amanar da aka bai wa shugaban makarantar, kari a kan rashin da’a da biyayya ga umarnin gwamnati.”

Kwamishinan ya kuma umarci shugaban makarantar da ya gabatar da kansa a Ma’aikatar Ilimin, inda daga nan kuma za a san mataki na gaba da za a dauka a kansa.

An kuma tattaro cewa za a maye gurbin Sabo Muhammad da wani babban jami’i a Hukumar Kula da Makarantun Sakandire ta Jihar.

Da farko dai wamnatin Jihar Kano ta umarci duk makarantun kwana a kan kada su bayar da hutun Sallah ga daliban da ke zana jarrabawar ta NECO.

Kara karanta wannan

Badaru Ya Buƙaci Musulmi Su Yi Addu’a Domin Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

A kan haka ne gwamnatin ta yi wa makarantun kyakkyawan tanadi na abinci, ciki har da sayen shanu 19 domin su yi shagalin Sallar a makaranta.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi

A cewar Kwamishinan, gwamnati ta yi wa daliban duk wani tanadi na gudanar da shagalin Sallah a makarantun cikin annashuwa da jin dadi.

A wani laarin kuma, wamnan jihar Jigawa Mohammadu Badaru ya bukaci al'ummar musulmi su yi amfani da damar salla babba (Ed-el-Kabir) domin yin addu'ar kawo karshen kallubalen tsaro da ke adabar kasar, The Guardian ta ruwaito.

Mr Badaru ya yi wannan kirar ne cikin sakonsa na sallah mai dauke da sa hannun babban mataimakinsa na musamman kan jaridu, Ahmad Danyaro, da ya fitar a ranar Litinin a Dutse.

Ya ce lokacin babban sallar da ya yi dai-dai da lokacin da aka kammala aikin Hajji a kasa mai tsarki babban dama ce ga yan Nigeria su yi addu'a ga Allah domin samun zaman lafiya a kasar.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Gwamnatin Ganduje Ta Sallami Shugaban Makaranta Saboda Hutun Sallah

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng