Bayani dalla-dalla: Yadda ake za ka nemi aiki a hukumomin Gwamnatin Tarayya uku da ke daukar aiki a yanzu

Bayani dalla-dalla: Yadda ake za ka nemi aiki a hukumomin Gwamnatin Tarayya uku da ke daukar aiki a yanzu

Akalla hukumomin gwamnati uku: Sojan Kasa da Sojan Sama da kuma FRSC, sun tallata guraben aiki a kwanan nan

Domin tabbatar da ‘yan Najeriya masu sha'awar neman guraben mukamai ba su fada hannun 'yan damfara ba, wannan shafi yana bayani dalla-dalla kan hanyoyin da za ka nemi guraben ayyukan cikin sauki.

Sojin Kasa na Najeriya

Sojin Kasa na Najeriyar na karbar takardun neman daukar aiki na kuratan sojin karo na 81.

Don kauce wa mazambata, hukumar tsaro ta saukaka abubuwa ta hanyar samar da cibiyoyi na zahiri a dukkan jihohi 36 na tarayyar Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

An fara daukar aikin sojin ne a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, kuma za a rufe a ranar Asabar, 24 ga watan Yuli, a cewar rundunar sojin kasan.

Don neman aikin, ga jerin cibiyoyin daukar aikin sojin:

Bayani dalla-dalla: Yadda ake za ka nemi aiki a hukumomin Gwamnatin Tarayya uku da ke daukar aiki a yanzu
Bayani dalla-dalla: Yadda ake za ka nemi aiki a hukumomin Gwamnatin Tarayya uku da ke daukar aiki a yanzu Hoto: HQNigerian Army
Asali: Facebook

Sojin Sama na Najeriya

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fara farautar makasan Janar din Sojan Kasa

Haka nan, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) tana neman wadanda suka kammala karatun digiri na farko da na biyu domin shiga aikin sojin a matsayin kananan hafsoshin 'Cadets Service Short Cadets'.

An bude shafin intanet domin cike gurbin neman aikin a ranar 26 ga watan Yuli za a rufe ranar Litinin 30 ga watan Agusta.

Don neman wannan aikin, ba ku bukatar ziyartar dukkanin wani shafin sada zumunta na zamani. Abin da kawai ya kamata ka yi shi ne ka ziyarci shafin intanet na rundunar mayakan saman wato NAF.

Haka nan, masu sha'awar shiga aikin za su iya kiran wadannan layukan domin taimaka musu daga 9:30 na safe zuwa 5:30 na yamma, tun daga ranar Litinin zuwa Juma'a, 09064432351, 08043440802, 09055840142 ko ta Email: caeers@airforce.mil.ng idan mutum yana bukatar karin bayani.

Sai dai ya kamata su kuma fahimci cewa aikin shiga a yi maka rajistar kyauta ne. Kuma dole ne masu neman aikin su kasance ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 8 da ya dace a sani game da marigayi Manjo Janar Ahmed

Dole ne ya kasance ba su wuce tsakanin shekara 20 zuwa 30 nan da 30 Satumba 2022.

Wadanda ke neman matsayin kwararrun likitoci dole ne su kasance tsakanin shekara 25 - 40.

Danna nan domin samun cikakken jerin abubuwan da ake bukata wajen cikewar.

Hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC

Har ila yau, Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) tana daukar ma’aikata na matsayi guda uku:

1: Officer Cadre

2: Marshal Inspectorate (MI) cadre

3: Road marshal assistant cadre

Don samun karin bayani, ziyarci shafin hukumar FRSC, www.recruitment.frsc.gov.ng.

Ana sa ran masu neman mukamin Officer Cadre su zama sun mallaki digiri na farko da shaidar kammala NYSC kuma dole ne ya zama mutum bai wuce shekara 30 ba.

Danna nan don cikakken jerin bukatar cancantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel