Da dumi-dumi: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba a matsayin hutu
- Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Talata, 20 ga Yuli da Laraba 21 ga watan Yuli a matsayin ranakun hutu don bikin babban sallah
- Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya bayyana hakan a yau Alhamis, 15 ga watan Yuli
- Ya taya daukacin al’umman Musulmai da ‘yan Najeriya na gida da waje murna
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Talata, 20 ga Yuli da Laraba 21 ga watan Yuli a matsayin ranakun hutu don bikin Eid-el-Kabir na bana.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya a yau Alhamis, 15 ga watan Yuli.
KU KARANTA KUMA: Bidiyo ya bayyana yayin da jama'a suka yi tururuwan fitowa don tarbar Shugaba Buhari a Kano
Ya taya daukacin al’umman Musulmai da ‘yan Najeriya na gida da waje murnar bikin na babban sallah.
Ya ce:
“Ina kira ga Musulmai da su ci gaba da nuna halin kauna, zaman lafiya, alheri da sadaukarwa, kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar sannan kuma su yi amfani da lokacin wajen yin addu’a don samun zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da kwanciyar hankali a kasar, duba da kalubalen rashin tsaro da muke fuskanta a wannan lokacin. Wadannan galibi sun kasance 'yan fashi a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas, masu satar mutane, 'yan fashi da makami, masu tayar da fitina na kabilanci da masu aikata miyagun laifuka a sauran sassan kasar."
Channels TV ta ruwaito cewa Ministan, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Sakataren Ma’aikatar, Dakta Shuaib Belgore, ya ba da tabbacin cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin kowane dan Najeriya.
wabin ya kuma ce gwamnati ta mayar da hankali ga tallafawa ‘yan kasa don samun nasarar rayuwa, abubuwan da aka tanada na shirye-shiryen saka jari da samar da cikakken tsaro a makarantu, musamman ma yadda ake yawan fuskantar matsalar satar yara 'yan makaranta.
Aregbesola, yayin da yake taya musulmai murnar bikin Eid-el Kabir, ya shawarci dukkan ‘yan Najeriya da su dauki alhakin kai rahoton duk wasu mutane da suke zargi da aikata laifuka ga jami’an tsaro, musamman a yayin wannan bikin.
Ya kuma yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su kiyaye matakan kare kai daga cutar Covid-19, musamman ta hanyar sanya takunkumin fuska, wanke hannu da nisantar jama'a domin kiyaye yaduwar cutar.
KU KARANTA KUMA: Jama’a sun fusata yayin da gwamnatin jihar Taraba ta fara siyar da fom din daukar aiki
"Dole ne dukkanmu mu dauki alhakin shawo kan cutar a yayin bikin na bana," in ji shi.
A wani labarin, masarautar Daura da ke Jihar Katsina ta bayyana cewa an dakatar da Hawan Sallah a bikin Babbar Sallah da za a yi saboda matsalar rashin tsaro da ake fama da shi.
A cikin wata sanarwa da Danejin Daura, Abdulmumini Salihu ya fitar ranar Talata, 13 ga watan Yuli, ya ce Mai martaba Sarki Umar Faruq Umar ya ɗauki matakin ne saboda matsalolin tsaro da suka addabi yankin masarautar, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.
A ranar 20 ga watan Yuli wanda ya yi daidai da ranar 10 ga watan Zul Hijja na shekarar Hijira ta 1442 ne daukacin Al’umman Musulmi za su gudanar da bikin Babbar Sallah.
Asali: Legit.ng