Nasrun minallah: Dakarun soji sun bindige 'yan Boko Haram 3, sun cafke 11 Borno

Nasrun minallah: Dakarun soji sun bindige 'yan Boko Haram 3, sun cafke 11 Borno

  • Wasu miyagun 'yan ta'addan Boko Haram sun rasa rayukansu yayin da wasu ke hannun dakarun soji
  • Sojojin Najeriya ne suka kai musu samame a wani yanki mai kusanci da Banki kan babbar hanyar Miyanti dake jihar Borno
  • Hakazalika, dakarun sun samu wasu miyagun makamai bayan bindige 'yan ta'addan da suka yi tare da kama wasu

Dakarun sojin Najeriya sun sheke wasu mutum uku da ake zargin 'yan Boko Haram ne tare da damke wasu 11 a cikin kokarin kawo karshen ta'addanci da suke yi a yankin arewa maso gabas.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasan, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce an sun fatattaki 'yan ta'addan wurin Banki kan babban titin Miyanti inda suka hana 'yan ta'addan wucewa tare da miyagun makamansu.

KU KARANTA: NAF: Rundunar sojin sama ta magantu kan labarin sabon hatsarin jirgin sama a Kaduna

Kara karanta wannan

Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

Nasrun minallah: Dakarun soji sun bindige 'yan Boko Haram 3, sun cafke 11 Borno
Nasrun minallah: Dakarun soji sun bindige 'yan Boko Haram 3, sun cafke 11 Borno. Hoto daga Nigerian Army
Asali: Facebook

KU KARANTA: An kama miyagun da suka yi garkuwa da mahaifin tsohon gwamna a jihar Filato

An kama 'yan ta'addan a ranar 15 ga watan Yulin kuma sun mika kansu tare da iyalansu bayan cigaba da ruwan bama-bamai da aka yi musu a maboyarsu.

An kama su ne a wuraren kauyukan Aza da Bula Daloye a karamar hukumar bama ta jihar Borno. Dakarun dake yankin Miyanti da Darajamel dake arewa maso gabas ne suka yi aikin.

"Wadanda ake zargin da aka kama sun hada da 'yan ta'adda maza 11, mata 5 da yara kanana 12," takardar tace.

"Dakarun sun samu carbi 27 na harsasai, AK47 guda 3 da rigar kare hari. A halin yanzu an fara bincikar wadanda ake zargin."

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kano ta soke dukkan hawan gargajiya tare da shagulgulan babbar sallah a wannan shekarar, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Matukin jirgin NAF ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka harbo jirgi

Wannan matakin na zuwa ne bayan mako daya da kwamitin fadar shugaban kasa na lura da korona ya bayyana wasu jihohi shida da suka hada da Kano a cikin jihohin da za a iya samun barkewar cutar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammadu Garba wanda ya sanar da hakan yace za a yi sallar idin babbar sallah ne a dukkan masarautu biyar da kuma masallatan dake fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel