Kotun Najeriya ta yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum

Kotun Najeriya ta yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum

  • Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom da ke zaune a karamar hukumar Ikot Ekpene ta jihar ta kammala sauraren karar garkuwa da wani dillalin shanu da ke Uyo
  • Mai shari'a Isangedighi ta bayyana dalilin da ya sa aka sami 'yan sanda biyu da wasu abokan aikinsu uku da laifin yin garkuwa da mutane
  • Jihohi da dama a fadin tarayyar kasar sun kafa dokoki da ke sanya hukuncin kisa ga satar mutane

Babbar kotun jihar Akwa Ibom ta yanke wa wasu ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda yin garkuwa da wani dillalin shanu mazaunin Uyo, mai suna Alhaji Muhammed Umar Barkindo.

‘Yan sandan da aka yanke wa hukuncin sun hada da Kofur Friday Udo, da kuma Saturday Okorie wadanda tuni aka sallame su daga rundunar ‘yan sanda ta Najeriya, jaridar The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka: Dalilin da yasa Gwamnan Zamfara ba zai sauka daga kujerarsa ba, Jigon APC

Kara karanta wannan

Yan ta'addan IPOB na shirin kai hari gidan yarin Kuje don kubutar da Nnamdi Kanu

Kotun Najeriya ta yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum
An yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Facebook

Kotun da ke zaune a karamar hukumar Ikot Ekpene ta jihar ta kuma yanke hukuncin kisa ga wasu mutum uku, Walter Udo, Ibiono Ibom, da Udo Etim wadanda aka yi amfani da gidansu don ajiye wanda aka yi garkuwa da shi, yayin da suke neman fansar naira miliyan 100.

Mai gabatar da kara ya tabbatar da shari'arsa yadda ya kamata

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa alkalin kotun, Justice Isangedighi, tace an yankewa wadanda ake zargin hukuncin kisa ne kamar yadda sashi na 1 (2) na dokar tsaron cikin gida ta jihar Akwa Ibom ta shekarar 2009 ta tanada.

Ta ce:

“Mai gabatar da kara ya tabbatar da shari'arsa ba tare da shakku ba kuma an sami wanda ake zargin da laifin hada baki da kuma sace Alhaji Muhammad Umar Barkindo a ranar 25 ga Nuwamba, 2011, laifin da ke da hukuncin kisa a Sashe na daya karamin sashe na biyu na Tsaron Cikin Gida na Jihar Akwa Ibom da Tilasta Bin Dokoki 2009. ”

Kara karanta wannan

Kotun Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Matawalle saboda sauya sheka zuwa APC

Mai shari'a Isangedighi ta roki Allah da ya tausaya wa wadanda aka yanke wa hukuncin.

Gwamnatin Neja ta gyara dokar kisa, an sa hannu a fara rataye masu garkuwa da mutane

A wani labarin, mai girma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sa hannu a kudirin da za ta bada dama a rika kashe masu garkuwa da mutane da barayin shanu.

A cewar jaridar The Cable, duk wanda aka samu da laifin satar mutum da nufin karbar kudin fansa a Neja, zai bakuncin barzahu ta hanyar rataye shi.

Abubakar Sani Bello ya ce an yi wa dokar garkuwa da mutane da satar dabbobi ta shekarar 2016 kwaskwarima domin a kashe masu ba miyagu bayanai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng